Aminiya:
2025-04-30@17:52:09 GMT

An shiga zaman ɗar-ɗar yayin da sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Ribas

Published: 19th, March 2025 GMT

Mazauna sun shiga zaman ɗar-ɗar a yayin da motocin yaƙi na sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Jihar Ribas.

Wannan dai na zuwa ne jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar.

Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Jihar Ribas

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa fiye da motocin soji 10 aka hanga suna sintiri a kan hanyar zuwa gidan gwamnatin yayin da wasu motocin yaƙi masu sulke suka tsaya wuri-wuri a hanyar.

Majiyar ta ce titunan birnin na Fatakwal sun zama fayau a yayin da mazauna suka tsere gidajensu.

Babu tabbaci ko gwamnan da aka dakatar, Similanayi Fubara yana cikin gidan gwamnatin a halin yanzu.

Sai dai majiyoyi sun ce akwai yiwuwar gwamnan ya samu labarin cewa za a ayyana dokar ta ɓacin tun kafin faruwar lamarin.

Bayanai sun ce gwamnan ya shafe tsawon wunin wannan rana ta Talata yana ganawa da ’yan majalisar zartarwarsa.

A halin yanzu dai birnin na Fatakwal ya zama fayau a yayin mazauna da ’yan kasuwa duk sun koma gidajensu.

Dalilin da Tinubu ya ayyana dokar ta ɓacin

Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi tare da kuma da naɗa wanda zai riƙe muƙamin gwamnan jihar na tsawon wata shida.

Tinubu ya sanar da matakin ne a wani jawabi da ya yi ta kafafen talabijin na ƙasar da yammacin ranar Talata.

A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi nuni da yadda aka rushe ginin majalisar dokokin jihar watanni 18 da suka gabata, wadda aka kasa sake gina ta har zuwa wannan lokaci.

“Jihar ta tsaya cik tun bayan ɓarkewar rikicin siyasar inda aka tauye wa al’ummar jihar hakkinsu na cin moriyar mulkin dimokuraɗiyya.

“Na yi iyakar bakin ƙoƙarina wajen ganin yadda za a magance matsalar to amma duka ɓangarorin sun yi watsi da yunkurin.

“Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Rivers, ya zama wajibi na yi amfani da sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999.

“A kan haka, na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025.

“Da wannan bayani, gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa Mrs Ngozi Odu da kuma dukkanin zaɓaɓbun ƴanmajalisar dokokin Jihar Ribas, an dakatar da su na wata shida, a matakin farko.

“A halin yanzu, na naɗa Vice Admiral Ibokette Ibas a matsayin wanda zai gudanar da lamurran jihar, domin amfanin al’ummar jihar,” in ji Tinubu.

Sai dai a cikin jawabin nasa, Tinubu ya bayyana cewa wannan doka da ya ƙaƙaba ba ta shafi ɓangaren shari’a na jihar ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Dokar Ta Ɓaci Jihar Ribas Siminalayi Fubara a ayyana dokar ta

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Sin Za Ta Samar Da Dokar Da Ta Shafi Raya Kasa

Haka kuma za a aiwatar da dukkan abubuwan da aka dade ana yinsu cikin shirin raya kasa a hukumance.

 

Ana sa ran dokar za ta kara inganta tsare-tsaren da za su tabbatar da aiwatar da shirye-shiryen raya kasa da karfafa dacewar manufofin da suka shafi dukkan bangarorin tattalin arziki da juna. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Sokoto Ya Amince Da Sauya Wa Manyan Sakatarori 25 Ma’aikatu A Jihar 
  • Tinubu zai ziyarci Katsina
  • Talauci Da Rashin Ilimi Ne Ya Sa Ayyukan Boko Haram Ke Dawowa – Gwamnan Yobe
  • Shugaba Tinubu Ya Taya Sabon Firaiministan Kanada Mark Carney Murna
  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Shirya Fara Tantance ‘Yan Fansho
  • Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Na Iran Ya Ce: Maganar ‘Yan Sahayoniyya Rudu Ne Maras Amfani
  • Sojoji Sun Harbe Mutane Biyu Har Lahira Da Ake Zargi Ɓarayin Mota Ne A Filato 
  • Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
  • Jihar Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Aikin Hajjin 2025
  • Kasar Sin Za Ta Samar Da Dokar Da Ta Shafi Raya Kasa