Shugaba Tinubu Ya Dakatar Da Gwamnan Jihar Rivers Da ‘Yan Majalisar Dokokin Jihar
Published: 19th, March 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Jihar Rivers, inda ya dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, da mataimakiyarsa Ngozi Odu, da dukkan mambobin Majalisar Dokokin Jihar na tsawon watanni shida.
A wani jawabi da ya yi ga alummar kasa ta kafafen yada labarai a ranar Talata, Shugaban kasan ya bayyana cewa an dauki wannan matakin ne sakamakon rikicin siyasa wanda ya ki ci ya ki cinyewa a jihar, ya kuma hana gudanar da gwamnati yadda ya kamata kuma ya tauye wa jama’ar Jihar Rivers morar romon dimokuradiyya.
Shugaban kasan ya nuna damuwarsa kan “mummunan hali” da jihar ke ciki, wanda ya kara muni bayan rushewar ginin Majalisar Dokokin Jihar da gwamnan ya yi a ranar 13 ga watan Disambar 2023. A cewarsa, duk da kokarin da ‘yan Najeriya masu kishin kasa suka yi don samun sulhu, rikicin ya ci gaba da tsananta.
Da yake magana kan hukuncin Kotun Koli na ranar 28 ga Fabrairu, 2025, wanda ya zargi gwamnan da aikata ayyukan da suka saɓa wa kundin tsarin mulki da raina doka, Shugaban kasa ya ce, “Babu gwamnati a Jihar Rivers, domin bangaren zartarwa ya rushe majalisar dokoki kuma yana mulki tamkar mulkin danniya.”
Shugaban kasan ya kuma bayyana cewa ya samu rahotannin tsaro da ke nuna barazana ga kadarorin kasa, ciki har da lalata bututun mai da wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu biyayya ga gwamnan ne suka aikata, ba tare da daukar wani mataki don dakile su ba.
Shugaban kasan ya nada tsohon Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Ibokette Ibas (Rtd), a matsayin mai kula da harkokin Jihar Rivers. Ya bayyana cewa bangaren shari’a na jihar zai ci gaba da aiki kamar yadda ya saba, sannan sabon mai kula da jihar zai kasance yana tsara dokoki ne kawai da amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya.
Shugaban kasan ya nuna fatan cewa wannan mataki zai tilasta dukkan bangarorin da abin ya shafa a Jihar Rivers su bi dokokin mulki tare da dawo da zaman lafiya.
Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Dokar Ta Baci Shugaban kasan ya Jihar Rivers
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ko ɗansa zai naɗa shugaban INEC, APC sai ta faɗi zaɓen 2027 — Dalung
Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya ce duk wani yunƙuri da Shugaba Bola Tinubu, zai yi ba zai hana jam’iyyar APC faɗuwa a zaɓen 2027 ba.
Yayin wata hira da aka yi da shi a Jos, a Jihar Filato, Dalung, ya ce ko da Tinubu zai naɗa ɗansa Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC), ko matarsa ta zama Babbar Alƙalin Alƙalai ta Ƙasa, hakan ba zai taimaka wa APC ba.
Tsadar rayuwa ta sa ’yan Nijeriya na siyan abincin da ya lalace Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a KanoYa ce gwamnatin APC ta gaza, kuma ta jefa ‘yan Najeriya cikin ƙunci da yunwa ta hanyar manufofinta marasa kan gado.
Dalung ya ce: “Ko duk gwamnonin jihohi 36 za su koma APC, kuma Tinubu ya naɗa ɗansa shugaban INEC, sai sun faɗi a 2027. Wannan karon tsakanin talakawa da gwamnati ne.”
Ya ƙara da cewa ‘yan Najeriya su shirya wa zaɓen 2027 domin ƙalubalantar gwamnatin Tinubu wadda ta jefa su cikin yunwa, talauci, da rashin adalci.
Dalung, ya bayyana jam’iyyar APC a matsayin mafakar muggan ‘yan siyasa, inda ya ce jam’iyyar ba ta da tsari ko aƙida, kuma yawaitar masu sauya sheƙa zuwa cikinta zai haddasa mata rikici nan ba da daɗewa ba.
Ya bayyana dalilin ficewarsa daga APC zuwa jam’iyyar SDP, inda ya ce taron da suka yi da Tinubu ya ba shi kunya, domin shugaban bai fahimci matsalolin da suka tattauna ba.
Dalung, ya kuma soki shugabannin siyasar Najeriya gaba ɗaya, inda ya bayyana cewa suna tafiyar da ƙasar ne ta hanyar son kai.