Waiwaye: Jihohin Da Aka Taɓa Sanya Dokar Ta-ɓaci A Nijeriya
Published: 19th, March 2025 GMT
Dalilin wannan doka shi ne rikice-rikicen addini tsakanin Musulmai da Kiristoci a watan Satumba 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,000.
A Jihar Borno Ma An Taɓa Sanya Dokar, Amma Ba A Jihar Baki Ɗaya Ba
A shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a wasu ƙananan hukumomin jihohin Borno, Adamawa, da Yobe saboda yawaitar hare-haren Boko Haram.
A 2013, Jonathan ya faɗaɗa dokar ta-ɓacin zuwa ɗaukacin jihohin Borno, Yobe, da Adamawa sakamakon tsanantar matsalar tsaro.
Wannan mataki ya bai wa jami’an tsaro ƙarin iko domin dawo da zaman lafiya.
Sai Kuma Jihar Ribas a Yanzu
Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin shugabanci da matsalolin tafiyar da gwamnati.
Shugaban Ƙasa Yana Da Dama Bisa Doka
Sashe na 305 na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya na 1999 ya bai wa Shugaban Ƙasa damar ayyana dokar ta-ɓaci a wata jiha idan ana fuskantar matsalar tsaro ko rikicin shugabanci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: dokar ta ɓaci a
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 7 sun mutu a hatsarin mota a Jigawa
Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Jihar Jigawa ya yi sanadin mutuwar mutane bakwai ciki har da direban motar tare da jikkata wasu 11.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Shiisu Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya aike wa manema labarai a Dutse.
Anthony Joshua zai yi dambe da tauraron YouTube Jake Paul a Disamba Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da sace ɗalibai mata a KebbiYa ce hatsarin ya afku ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin Lahadi, 16 ga Nuwamba 2025, a ƙauyen Jigawan Kurma da ke kan titin Kiyawa zuwa Azaren Jihar Bauchi.
A cewar SP Shiisu, “Mota kirar Hummer ce da ta taso daga Kano zuwa Potiskum ɗauke da fasinjoji 18. Hatsarin ya faru ne bayan fashewar tayoyi biyu, sakamakon gudun wuce sa’a da direban yake yi.”
Ya ƙara da cewa sauran 11 da suka samu munanan raunuka an garzaya da su babban asibitin Birnin Dutse, inda aka sallami huɗu daga cikinsu bayan samun kulawa.