Babban Mashawarcin Tsaro na Kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa an kashe ’yan ta’adda sama da 13,000 a fadin Najeriya daga lokacin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hau mulki a watan Mayun 2023 zuwa yanzu.

Ribadu, yayin da yake jawabi a taron Koli na Jam’iyyar APC a zauren taro na Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ya bayyana cewa duk da an samu ci-gaba mai sosai wajen magance matsalar rashin tsaro, yanayin sarƙaƙiyar tsaro ya sa a mafi yawan lokaci jama’a ba sa iya gane waɗannan nasarori nan take.

Ribadu ya bayyana cewa an kashe jimillar ’yan tada kayar baya da ’yan fashin daji 13,543, yayin ayyuka daban-daban da sojoji da sauran hukumomin tsaro suka gudanar a faɗin ƙasar.

Ya ƙara da cewa mayaƙan Boko Haram da ISWAP 124,408 sun miƙa wuya ga jami’an tsaro.

Abin da muka sani kan labarin juyin mulki a Kwaddibuwa NAJERIYA A YAU: Dalilin ’Yan Adawa Na Ƙulla Ƙawance A Ƙarƙashin Inuwar ADC

“Tun da Tinubu ya hau mulki, lamarin ya canza, inda aka   kashe shugabannin ’yan ta’adda da yawa. Sojojinmu sun kashe ’yan ta’adda 13,543,” in ji Ribadu.

Ya bayyana kalubalen tsaro da gwamnatin yanzu ta gada a matsayin “wanda ke barazana ga haɗin kai da zaman lafiya da mutuncin Najeriya. Akwai manyan hare-hare, manyan barna da kuma asarar rayuka masu yawa.”

Ribadu ya lissafa manyan barazanar da suka kasance a lokacin, ciki har da “Boko Haram, ISWAP, fashi da garkuwa da mutane a Arewa maso Yamma, tayar da ƙayar baya a Kudu maso Gabas, Neja Delta da kuma rikicin makiyaya da manoma musamman a Arewa ta Tsakiya.”

Amma ya jaddada cewa duk da haka, an samu a fannin tsaro tun lokacin da gwamnatin yanzu ta hau mulki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan ta adda Boko Haram ISWAP Tsaro yan ta adda

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba

 

Danja ya ce, sojojin a yayin da suke aiki da sahihan bayanan sirri dangane da shirin kai hari kan al’ummar Chanchangi da kungiyar ta’adda ta Bojo ke shirin yi a ranar 15 ga Satumba, 2025, sun yi artabu da ‘yan ta’addan a kan hanyar Demeva zuwa Chanchangi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • An kama ɗaya daga cikin manyan kwamandojin IPOB
  • Yanzu-yanzu: Shugaba Tinubu Ya Ɗage Dokar Ta-ɓaci A Jihar Ribas
  • Lakurawa Sun Hallaka Jami’in Kwastam A Jihar Kebbi
  • Sojoji sun harbe mayaƙan ISWAP 8 a Borno
  • Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba
  • Kukan al’umma kan lalacewar hanyar Dukku
  • ’Yan ‘Mafiya’ na ƙoƙarin kashe matatar man fetur da na gina —Ɗangote
  • Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar