Aljeriya Ta Kori Jami’an Diflomasiyya Faransa 12
Published: 15th, April 2025 GMT
Gwamnatin kasar Ajeriya ta bayyana jami’an diflomasiyyar Faransa da suke kasar su 12 a matsayin ‘wadanda ba a bukatar ganinsu” a cikin kasar, tare da yin kira a gare su da su fice a cikin sa’oi 48.
Bugu da kari kasar ta Aljeriya ta yi suka da kakkausar murya akan ministan harkokin wajen Faransa Bruno Rotayo,tare da cewa za ta mayar masa da martanin da ya dace.
Sanarwar ma’aikatar harkokin wajen ta Aljeriya ta bayyana cewa; A matsayinta na kasa mai cikakken shugabanci, tana daukar ma’aikatan ofishin jakadanci Faransa 12 a matsayin wadanda ba a maraba da su, sannan kuma ana bukatar da su fice daga kasar a cikin sa’oi 48.”
Aljeriya din ta dauki wannan matakin ne a matsayin mayar da martani ga kama wani jami’in diflomasiyyarta da aka yi a kasar Faransa a ranar 8 ga watan Aprilu da ake ciki.
Aljeriyan ta bayyana abinda ya faru da cewa, keta hurumin kasarta ne da kuma take dokokin aikin diflomasiyya.”
Haka nan kuma ta yi ishar da cewa, ma’aikacin diflomasiyyar da aka kama yana da kariya ta aiki wacce ta hana a yi masa abinda ya faru,amma kuma gwamnatin Faransa ta yi mu’amala a shi ta hanya mafi muni da halayya irin ta barayi.’
Alaka a tsakanin Faransa da Aljeriya tana kwan-gaba da baya, musamman a cikin watannin bayan nan. Watanni 8 da su ka gabata an sami rashin jituwa a tsakaninsu saboda korar wasu ‘yan asalin Aljeriya mazauna Faransa bisa zargin cewa sun shiga kasar ba bisa ka’ida ba. Aljeriya ta yi wa jakadanta kiranye, tare da rufe kafar diflomasiyya a tsakaninsu na tsawon watanni 8.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Aljeriya ta
এছাড়াও পড়ুন:
An Fara Baje Kolin Kayakin Da Ake Kerawa A Iran Tare Da Taron Iran Da Afirka Karo Na Uku
An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya fadawa kamfanin dillancin labaran IP kan cewa Kasuwar ta bana dai, za ta tara kamfanonin masu samar da kayaki daga yankuna daban daban na kasar Iran da dama, kuma akwai fatan cewa wannan kasuwar ta zama mabudi ga kyautatuwan tattalin arzikin kasar.
EXPO dai ita ce kasuwar baje koli na kayakin kasar Iran mafi girma wanda ake gudanarwa a ko wace shekara, sannan daga nan take samun kasuwa a kasashen duniya. Kuma yan kasuwa daga kasahe fiya da 100 ne suka shigo kasar don halattan kasuwar.
Esma’il Bakaee, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ce ya na fatan a wannan kasuwar, kasashen Afirka da Iran za su amfani juna a harkokin kasuwancin da ake bunkasa a tsakaninsu.