’Yan bindiga sun kai hari a kan taron masu ibada inda suka yi awon gaba da mutane da dama da ba a tantance ainihin yawansu ba.
Mutane suna tsaka da gudanar da ibadar dare ne a kan wani tsauni a lokacin da ’yan bindigar suka kai musu farmakin suka yi garkuwa da su.
Lamarin ya auku ne a ranar Juma’a yankin Egbola, a kan hanyar Agabja a Ƙaramar Hukumar Lokoja.
Shaidu sun bayyana cewa ’yan bangan gwmanatin jihar sun yi nasarar ceto wata mata daga cikin masu ibadan, bayan sun samu rahoton aukuwar lamarin.
NAJERIYA A YAU: Dalilan Rikice-Rikice A Jihar Filato Yadda kisan mutum fiye da 50 a Filato ya tayar da ƙuraWani ɗan banga daga cikin waɗanda suka kai ɗauki ya bayyana cewa matar ta tsere ne bayan da ’yan bindigar suka kawo harin, daga bisani ’yan bindigar suka tsince ta.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin yin magana da mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Kogi, ASP William Aya, amma jami’in bai amsa ko ɗaya daga cikin kiraye-kirayen wayan wakilin namu ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga awon gaba Garkuwa ibadar dare Jihar Kogi
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnonin Arewa Za Su Zuba Biliyoyin Naira Don Yaki da Matsalar Tsaro
Daga Aliyu Muraki
Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce gwamnonin Arewa sun amince su sayi na’urorin zamani na tsaro da kuma daukar matasa aiki don tallafawa ayyukan tsaro domin magance matsalolin rashin tsaro a yankin.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Jihar da aka gudanar a Lafia, babban birnin jihar.
Gwamna Abdullahi Sule, wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Arewa ta Tsakiya, ya ce an cimma wannan matsaya ce a taron gwamnonin Arewa da aka yi a Kaduna kwanan nan.
A cewarsa, gwamnonin Arewa sun amince cewa kowace jiha za ta rika bada gudummawar Naira Biliyan Daya a kowane wata na tsawon shekara guda domin samar da kudin da zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro a yankin.
Ya ce kwamitin gwamnonin Arewa zai gina sakatariyarsa a Kaduna, inda gwamnonin Arewa goma sha tara suka bayar da Naira Miliyan Dari Dari na tsawon shekara guda.
Gwamna Abdullahi Sule ya kuma yi karin bayani kan dakatar da ayyukan hakar ma’adinai a jihar Nasarawa, inda ya bayyana cewa wannan dakatarwar ba haramta dukkan ayyukan hakar ma’adinai na tsawon watanni shida ba ce, an dakatar da bayar da sabbin lasisi ne, har sai an kammala tantance sahihan masu hakar ma’adinai.
Manufar tantancewar ita ce gano masu hakar ma’adinai na gaskiya da kawar da masu hakar ma’adinai na fasa-kwauri wadanda ba sa kawo kudaden shiga ga jihar, tare da haifar da matsalolin tsaro.
Gwamnan ya bayyana cewa kasancewar masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba a jihar ta zama mafakar ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro, wanda hakan ya sa aka bukaci tsauraran dokoki da ingantaccen tsari.