HausaTv:
2025-04-30@23:24:52 GMT

Trump, ya ce ya yi tattauna mai armashi da Zelensky, bayan wacce ya yi da Putin

Published: 19th, March 2025 GMT

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada ya bayyana a wannan Laraba cewa ya yi tattaunawa mai kyau” da Volodymyr Zelensky, washegarin da ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin.

Ya kara da cewa tattaunawar ta yi armashi yayin da Amurka ke yunkurin tsagaita wuta a Ukraine.

“Na yi magana da shugaban Ukraine Zelensky, ta dauki kusan awa daya, kuma galibin tattaunawar ta ta’allaka ne kan kiran da suka yi da shugaba Putin na jiya domin daidaita batun kasashen Rasha da Ukraine, kuma  “Muna kan hanya madaidaiciya,” inji shugaban na Amurka a shafinsa na True Social Network.

Tunda farko dama wakilin Amurka Steve Witkoff ya bayyana a ranar Talata bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin game da haduwar birnin Jeddah na kasar Saudiyya kan shirin tsagaita bude wuta a Ukraine.

Bayanai sun nuna cewa tawagar Amurkan da za ta je Saudiyya za ta kasance karkashin jagorancin sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio da kuma mai ba da shawara kan harkokin tsaro Mike Waltz, amma ba wai wadanda za su shiga tsakani ba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Al-Shara Ya Ki Abincikewa Da Tsarin Tarayya Wanda Kurdawan Kasar Siriya  Suke Bukata

Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan  kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab.

Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan kasar ta Siriya sannan tsarin tarayya ya sabawa yarjeniyar da aka kulla da kurdawan a baya-bayan nan.

A wani taron da suka gabatar a makon da ya gabata,  jam’iyyar kurdawan kasar ta Siriya (SDC) ta fadawa “ The National  ”  bayan taron kan cewa suna bukatar tsarin tarayyar a kasar Siriya don shi ne kadai zai tabbatar da hakkinsu a kasar.

A cikin watan maris da ya gabata ne shugaba Al-Sharaa na kasar Syriya ya rattaba hannu a kan wata yarjeniya da shugaban dakarun kurdawan kasar Siriya SDF Mazlum Abdi dangane da hade dakarunsa da sojojin kasar Siriya, sannan yace tsarin tarayya ya sabawa wannan yarjeniyar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araghchi : Za’ayi Tattaunawar Iran da Amurka ta gaba a Rome bayan taron E3
  • Kar A Mika Wuya Ga “Damisar Takarda”
  • Yanayin Rudani Na Tsawon Kwanaki 100 Kashedi Ne Ga Amurka
  • Karin Wata Kasa Da Bai San Ta Ba A Doron Duniya
  • Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba
  • Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Sa’o’ii 72
  • Majalisar Dinkin Duniya Ta Jaddada Wajabcin Komawa Kan Shirin Tsagaita Bude Wuta A Gaza
  • Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine
  • Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Alhazan Jihar Kwara A Ranar 12 Ga Watan Mayu
  • Al-Shara Ya Ki Abincikewa Da Tsarin Tarayya Wanda Kurdawan Kasar Siriya  Suke Bukata