Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa
Published: 12th, March 2025 GMT
Wasu ’yan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai hari garin Farin Duse da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa, inda suka kashe wata mata juna, Azumi Allah Gaba, tare da wasu mutum 10.
Binciken Aminiya ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da wani makiyayi ke kiwon shanunsa, ya yanke wata bishiyar mangwaro domin ciyar da dabbobinsa.
Wani mazaunin yankin ya yi ƙoƙarin hana shi, lamarin da ya haifar da cacar baki a tsakaninsu.
Makiyayin ya harbe mutumin nan take, wanda hakan ya haddasa mummunan rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoman Gwari.
Wani ganau da ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa: “Rikicin ya fara ne da misalin ƙarfe 6 na safe a ranar Lahadi, 9 ga watan Maris, 2025, har zuwa yammacin Talata.
“Jami’an tsaro sun tabbatar da zaman lafiya, amma har yanzu garin Gwari babu kowa, kuma ana jin harbe-harbe a Farin Ruwa Duse.”
An ƙone gidaje sama da 20 tare da lalata wani ofishin ’yan sanda da ke yankin.
Wasu bayanai sun nuna cewar an lakaɗa wa DPO duka, sannan aka lalata babur ɗinsa.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa, ta tabbatar da mutuwar Azumi Allah Gaba da jaririnta da ke cikinta, tare da wasu mutane.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Nansel Rahman, ya fitar, ya bayyana cewa an kama wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a rikicin.
Ya tabbatarwa da jama’a cewa jami’an tsaro sun shawo kan lamarin, kuma ana ci gaba da bincike don kama waɗanda suka aikata laifin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Makiyaya Nasarawa
এছাড়াও পড়ুন:
Mutanen unguwa sun kama masu ƙwacen waya a Kano
Al’ummar yankin Bachirawa a Jihar Kano sun yi ta maza sun cafke wasu matasa biyu da ake zargi da ƙwace waya a unguwar a yayin da ɓata-garin suke tsaka da ƙwacen.
Matasan dai sun tare wata mata ce a unguwar suka ƙwace mata waya, wanda hakan ya sa mutanen yankin suka yi kansu tare da kama su.
An samu nasarar karɓe wayar da suka amsa tare da ƙwace makaman da aka samu a hannunsu.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya sanar da haka bayan al’ummar sun miƙa waɗannan matasa ofishin ’yan sanda a ranar Juma’a.