HausaTv:
2025-07-02@02:29:37 GMT

EU ta jadadda bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomasiyya

Published: 12th, March 2025 GMT

Kungiyar tarayyar turai ta jaddada bukatar warware batun Iran ta hanyar diflomatsiyya.

Da taek sanar da hakan babbar Jami’ar kula da harkokin ketare ta kungiyar ta ce babu wata hanyar da za’a bi wajen warware matsalar Iran in ba ta diflomasiyya ba.

‘’ta hanyar diflomatsiyya ne za’a warware takaddamar da ake game da batun yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015 da iran, inji Kaja Kalas.

Da take magana a taron shekara-shekara na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan hadin gwiwa tsakanin EU da Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York, babbar jami’ar ta Tarayyar Turai ta ce “ci gaba da fadada shirin nukiliyar Iran ya sabawa alkawurran da Iran ta dauka kamar yadda kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shi.

“A lokaci guda kuma, hanyar da ta shafi bangarori daban-daban, kamar yarjejeniyar, tana da mahimmanci.

Ta ce, “Babu wata hanyar da za ta dore wajen warware matsalar sai ta diflomasiyya,” in ji ta, a cewar shafin yanar gizon EU External Action.

A kwanan ne dai shugaban AMurka Donald Trump, y ace ya aike da wasiga ga Iran, na ta bude tattaunwa ko kuma ya yi da karfin soji.

Iran dai ta musanya samun wata wasika daga Trump, kuma tana mai cewa babu batun tattaunawa bsia matsin lamba da barazana.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda, Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wakilan Kasashen Duniya Da Kungiyoyin Sun Je Ta’aziyya Mutanen Da Suka Yi Shahada A Yakin Iran Da H.K.Isra’ila
  • Fahimtar Sabon Tunani: Yadda Sin Ta Samu Bunkasa A Tarihi Ta Hanyar Juyin Juya Halin Da Take Yi Wa Kanta 
  • Iran Ta Ce Babu Batun Tattaunawa Duk Tare Da Amurkawa Sun Ce Za’a Yi
  • Xi Ya Jaddada Bukatar Yin Aiki Tukuru Wajen Aiwatar Da Jagorancin Jam’iyya Bisa Kyawawan Akidu
  • Isra’ila na neman ƙulla hulɗa da Siriya da Lebanon
  • Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa
  • Riƙaƙƙen Ɗan Ta’adda, Bello Turji, Yana Neman Ayi Sulhu Bayan An Kashe Yaronsa
  • Iran Ta Bukaci Gudanar Da Bincike Kan Dalilin Isra’ila Na Kai Harin Kan Gidan Yarin Tehran
  • Shugaban Majalisar Dokokin Jama’ar Kasar Mexico: Tunanin Raya Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ga Dukkan Bil’adama Da Shugaba Xi Jinping Ya Gabatar Ya Kayatar
  • Kalibof Ya Mayarwa Shugaban Kasar Amurka Martani Kan Mummunan Kalamansa