Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [4]
Published: 12th, March 2025 GMT
Wannan umurni yana da tushen shari’a daga Alƙur’ani da Hadisi, kuma yana da hikima da fa’ida da dama. Allah Ta’ala Ya umurci Musulumi da yin isti’aza kafin karanta Alƙur’ani kamar yadda Ya labarta mana haka a cikin Suratul Nahli a aya ta 98. Inda Ya ce:” To idan za ka karanta Alƙur’ani sai ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan korarre (daga rahamar Allah).
Ma’anar Isti’aza:
Isti’aza na nufin neman tsari da kariya da fake wa a wurin Allah Shi kaɗai ban da waninsa daga sharrin Shaiɗan. Domin ƙarin haske duba Ibnu Jarir; Jãmi’ul Bayãni [1/111], Ibnu Kasir; Tafsirul Kur’anil Azim [1/27], da Ibnul Ƙayyim; Badã’i’ul Fawã’id [2/200].
Yaushe ake Isti‘aza?:
Malamai sun yi saɓani dangane da lokacinda za a yi Isti‘aza, sai dai magana mafi ingani da malamai mafiya yawa suke a kanta shi ne ana yin Isti‘aza ne kafin a fara karatu. Domin ƙarin haske duba Ibnu Ibnu Juzai; Kitãbut Tashīl fi Ulūmil Kitãbi [1/30], da Bagawī; Ma’ãlumut Tanzīli [[5/42] da Ibnu Aɗiyya; al-Muharrul Wajizi [1/58], da Ibnul Jauzi; Zãdul Masīri [1/14].
Hukunci Isti‘aza Kafin Karanta Alƙur’ani:
Malamai mafiya yawa sun tafi a kan mustahabbi ne yin isti‘aza a lokacin karanta Alƙur’ani a wajen salla. Amma sun yi saɓani a wajen karatun salla, an hakaitu Imamu Malik ba ya isti‘aza a sallar farilla amma yana yi a sallar asham, shi sa ake yi a sallar nafila. Amma Imam Abu Hanifa da Imam Asshafi’i suna yi isti‘aza a sallar farilla. Akwai waɗanda suke ganin wajibi ne a yi isti‘aza a salla gaba ɗaya. Domin ƙarin haske duba Kitãbu at-Tashīlu fi Ulūmi at-Tanzil [1/30] da Ibnu Kasir; Tafsirul Kur’anil Azim [1/26] da al-Ƙurɗubi; al-Jãmi’u Li’ahkãmil Ƙur’ãni [1/86]
Hikimar Yin Isti’aza Kafin Karanta Alƙur’ani:
Akwai hikimomi masu tarin yaw na yin isti‘aza kafin karatu. Ga wasu daga cikinsu:
1. Kariya daga tasirin Shaiɗan: Shaiɗan yana hana mutum fahimtar Alƙur’ani kuma yana kuma sanya ruɗani. Yin isti’aza na kare mai karatu daga fitinarsa.
2. Tsaftace zuciya: Isti’aza kafin karanta karanta Alƙur’ani yana ba wa zuciya tsarki da nufin Allah a karatu da samin tsoron Allah, tare da tadabburi.
3. Bin sunnon Annabi (SAW): Domin Annabi (SAW) yana Isti’aza kafin ya fara karatu.
4. Tsaftace Baki: Yin isti‘aza yana tsaftace baki daga abuwan da ta aikata na wargi da yasasshen zance, domin shiga karanta maganar Allah cikin tsarki da tsafta.
Daga: Abu Razina, Nuhu Ubale Paki
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Abu Razina Nuhu Ubale Paki Ramadan isti aza kafin karanta Isti aza kafin karanta karanta Alƙur ani
এছাড়াও পড়ুন:
An Bude Kashi Na Uku Na Canton Fair Karo Na 137
Cibiyar cinikayyar kasashen waje ta kasar Sin, mai shirya bikin, ta ba da sanarwar cewa, baya ga wuraren baje kolin da suka shafi farfado da yankunan karkara da za a ba su rumfuna kyauta, sauran masu baje kolin kayayyakin da ake fitarwa zuwa kasashen waje su ma za a rage musu kudaden rumfunansu da kashi 50 cikin dari a wajen bikin Canton Fair karo na 137.
Ana gudanar da bikin Canton Fair karo na 137 ne a matakai uku, daga ranar 15 ga Afrilu zuwa 5 ga Mayu. Kashi na farko da na biyu sun jawo hankulan masu sayayya fiye da 220,000 daga kasashe da yankuna 219 na duniya, inda suka kafa sabon tarihi a lokaci guda.
Wannan ya nuna yadda kasuwancin kasashen waje na kasar Sin ya tsaya kyam da kafafunsa tare da karin kuzari, kana ya kara wa kamfanoni kwarin gwiwar yin bincike kan yadda za su ci gajiyar kasuwanni daban daban. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp