Adam A. Zango ya auri jarumar Kannywood
Published: 17th, August 2025 GMT
Fitaccen jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, Adam A. Zango ya agwance da jaruma Maimuna Musa.
Marubuciya a masana’antar, Fa’iziyya D. Sulaiman ce ta sanar da auren nasu a wani rubutu da ta wallafa a Facebook.
Wani mutum yanke makazutarsa a Borno Ta’aziyyar Sarkin Zuru: Muhammadu Sani Sami (1943-2025)Auren dai ya zo cikin bazata, domin babu wanda ya san da neman sai labari aka ji jaruman sun shiga daga ciki.
Jaruma Maimuna matashiya ce wadda tauraronta ya fara haskawa a Kannywood.
Ta yi fina-finai kamar Kwana Casa’in, Garwashi da sauransu.
A baya-bayan nan ma fitacciyar jaruma a masana’antar, Rahama Sadau, ita ma ta yi aure, lamarin da ya bai wa mutane da dama mamaki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Garwashi kannywood Kwana Casa in
এছাড়াও পড়ুন:
Dan Wasan Barkwanci A Finafinan Indiya, Asrani Ya Rasu
Fitaccen jarumin barkwancin finafinan Indiyan nan Asrani ra rasu.
Asrani, wanda asalin sunansa shi ne Govardhan Asrani, ya rasu yana mai shekaru 84, kuma ya shafe sama da shekara 50 yana fitowa a finafinan Indiya, inda ya fito a finafinai sama da 350.
Dan wasan finafinan, ya shahara wajen taka rawar barkwanci da kuma ƙaramin jarumi wanda ake kira da mai taimaka wa jarumi wato supporting actor. Daga cikin fina-finansa da suka yi fice akwai Sholay, inda ya fito a matsayin ɗansand da Bawarchi da Chupke-Chupke da Hera Pheri da Muqabla da Dhamaal da Yamla Pagla Deewana da Dillagi da Welcome da Bhool Bhulaiya da Garam Masala da Baghban da The Burning Train da Ajnabee da Seeta aur Geeta da Sargam da dai sauransu.
Ya karbi lambobin yabo da dama da suka hada da jarumin da yafi kowa iya barkwanci wanda kamfanin Film Fare ya ba shi.
Ya mutu ya bar matarsa wadda ita ma jaruma ce wato Manju Asrani da kuma ɗansa Naveen Asrani.
Ya yi fina-finai da jarumai da dama da suka hada Amita Bachchan da Dharamendra da Jeetandra da Shatugan Sinha da Rajesh Khanna da Rishi Kapoor da Vinod Khanna da Akshay Kumar, da Shahrukh Khan da Aamir Khan da Salman Khan da Ajay Devgan da Sanjay Dutt da dai sauransu.
Bbc