Dabarun Kasar Sin Na Iya Kawo Karshen Yunwa A Duniya
Published: 18th, March 2025 GMT
A baya-bayan nan yayin hira da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan kula da harkokin gona na kasar Gambiya Demba Sabally, ya bayyana goyon baya da taimakon fasaha na kasar Sin, a matsayin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da gagarumin ci gaba a fannin aikin gona a kasarsa a ’yan shekarun nan.
Idan ana batu na kirkira da amfani da fasahar zamani a duniya, to kowa ya san cewa kasar Sin ta yi zarra a wannan bangare. Haka kuma kowa ya san duk wani ci gaban da Sin take nema ko ta samu, tana yi ne domin jama’arta su kasance cikin walwala, shi ya sa ci gaban Sin a fannin kirkire-kirkiren fasahohin zamani, ya game kowane bangare na rayuwa, ciki har da ayyukan gona. Kasar Sin daya ce daga cikin kasashe mafiya yawan jama’a a duniya, amma jajircewarta da dabarunta, sun ba ta damar ciyar da daukacin al’ummarta, duk da cewa, ba ta da filin noma mai yawa.
Wakilin Musamman Na Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Rantsar Da Shugabar Namibiya Gwamna Yusuf Ya Yi Barazanar Ƙwace Lasisin Jerin Gidajen Kwankwasiyya, Amana Da BandirawoHakika dabarun Sin abun koyi ne, musamman yadda kasar ke jajircewa wajen ganin ta taimakawa kasashe masu tasowa. Yayin da ake fama da tarin matsaloli a duniya, ciki har da rashin abinci, rungumar dabarun da matakan kasar Sin ba makawa za su samar da wadatar abinci a duniya. Kasashe da dama sun gwada kuma sun samu sakamakon a zo a gani. Misali, dalilin kasar Sin da fasahar tagwaita irin shinkafa, kasar Madagascar ta cimma burinta na samun wadatar abinci, inda a yanzu yabanyar da ake samu ta rubanya ta baya fiye da sau 1. Ita ma kasar Gambia, yawan yabanyar da take samu na ci gaba da karuwa, inda yawan shinkafar da kasar ta samu a shekarar 2024 ya haura tan 48,000, adadin da ya kafa tarihi.
Har kullum, kasar Sin ta kasance mai rajin neman ci gaba na bai daya a duniya maimkon bai wa kanta fifiko. Hakan ne kuma ya sa take gabatar da dabaru da fasahohinta ga kasashe masu tasowa, wanda ke haska burinta na gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama, wanda muke sa ran za ta kai ga samar da wadata da zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin duniya. (Faeza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Ya kuma bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta gabatar da duk wani taimakon da JMI take bukata a yayin tattaunawar.
A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta IAEA kamar yadda yarjeniyar NPT take bukata da kuma dokokin kasa da kasa.
Abbas ya fada masa inda aka kai ya zuwa yanzu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, a biranen Mascat na kasar Omman da kuma Roma na kasar Italiya.
Ya zuwa yanzu dai kasashen biyu sun gudanar da taro har sau uku dangane da shirin Nukliyar kasar ta Iran, kuma bangarorin biyu sun bayyana amincewarsu da yadda tattaunawar take tafiya.