Shugaba Tinubu Ya Kafa Kwamitin Kidayar Jama’a Na Kasa
Published: 17th, April 2025 GMT
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da wani babban kwamiti kan kidayar jama’a da gidaje mai zuwa, inda ya umurci mambobin su gabatar da rahoton farko cikin makonni uku.
Shugaban wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan fadar sa, Femi Gbajabiamila, a wajen taron da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Abuja, ya ce kidayar na da matukar muhimmanci ga ci gaban kasa da kuma tsare-tsare na gaskiya.
Ya lura cewa ingantaccen bayanan yawan jama’a yana da mahimmanci don yanke shawara mai inganci a cikin manyan sassan kamar kiwon lafiya, ilimi, tsaro, da kuma tsara tattalin arziki.
Shugaban ya jaddada cewa, an gudanar da kidayar jama’a ta karshe a shekarar 2006, wato kusan shekaru ashirin da suka wuce, kuma tun daga lokacin ne Najeriya ta fuskanci sauye-sauye a yawan al’umma, matsugunan jama’a, da kuma muhimman abubuwan da suka shafi kasa baki daya.
Ya kuma jaddada mahimmancin tsarin da aka yi amfani da shi na fasaha don tabbatar da sahihin sakamako mai inganci, inda ya bayyana bukatar yin hadin gwiwa a tsakanin dukkanin hukumomin da abin ya shafa, da suka hada da hukumar kidaya ta kasa, da hukumar kula da shaida ta kasa NIMC, da ma’aikatar kudi, da ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan kidayar jama’a da gidaje kuma ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Sanata Atiku Bagudu, ya tabbatar da cewa kwamitin zai gabatar da rahotonsa cikin wa’adin makonni uku da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar.
Bello Wakili/Abuja
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Kwamiti kidayar jama a
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Mene ne tasirin naɗin Mataimaka na Musamman a rayuwar jama’a?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Zaɓaɓɓun shugabannin gwamnati sukan naɗa wasu muƙarrabai don su taya su sauke nauyin da aka ɗora musu.
Wasu na zargin naɗin ba ya rasa nasaba da sakayya ga irin rawar ga waɗanda aka naɗa saboda rawar da suka taka yayin yaƙin neman zabe.
Shin irin waɗannan nade-naɗe na da wani tasiri ga rayuwar al’umma?
NAJERIYA A YAU: Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan Najeriya Kitse Daga Wuta? DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke HaifarwaShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nade-naɗen masu taimaka wa shugabanni da irin tasirin da suke da shi.
Domin sauke shirin, latsa nan