Iran Ta Damu Akan Mummunan Yanayin Da Mutanen Al-Fasha Na Sudan Suke Ciki
Published: 17th, April 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana cewa; Yanayin da mutanen garin al-fasha na Sudan suke ciki ya yi muni, tare da yin kira da a kawo karshe killace garin da aka yi da kuma bai wa fararen hula kariya.
Mayakan “Rundunar Kai Daukin Gaggawa” dake fada da sojojin Sudan ta shimfida ikonta akan sansanin ‘yan hijira na “Zamzam’ bayan kwanaki na barkewar fada a kusa da birnin al-fasha.
Daruruwan mutane ne su ka rasa rayukansu yayin da wani adadi mai yawa na ‘yan hijirar ya jikkata.
Dr. Isma’ila Baka’i ya bayyana matsayar jamhuriyar musulunci ta Iran na nuna cikakken goyon bayan Sudan a matsayin dunkulalliyar kasa.
A bisa kididdigar MDD a kalla mutane 300 aka kashe a kusa da wannan sansanin na Zamzam a fadan da aka yi a ranakun Juma’a da Asabar.
Har ila yau MDD ta kuma ce,wani adadin na mazauna yankunan Zamzan da Abu Shok da garin al-Fashar da sun kai 400,000 an tilasta musu ficewa daga gidajensu. Haka nan kuma wasu mutanen da sun kai miliyan 13 sun gudu, zuwa inda za su sami aminci a cikin gida da kuma wajen kasar.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Mutanen da talauci ya yi wa katutu zai ƙaru a Nijeriya — Bankin Duniya
Bankin Duniya ya yi hasashen cewa adadin waɗanda talauci ya yi wa katutu a Nijeriya zai ƙaru zuwa kaso 3.6 cikin ɗari a 2027.
Wannan dai na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar game da tattalin arziki da kuma yanayin tsadar rayuwa a Nijeriya.
Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura a Sifaniya da Portugal Talata ce ɗaya ga watan Zhul Qi’ida — Sarkin MusulmiBankin Duniya ya fitar da rahoton ne bayan ganawa tsakanin wakilansa da na Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF kamar yadda RFI ya ruwaito.
Rahoton ya ce dogaro da Nijeriya ta yi gaba ɗaya kan man fetur na ɗaya daga cikin dalilin da zai sa haɓakar tattalin arzikinta ya ci gaba da tafiyar hawainiya.
Bankin Duniyar ya ce har yanzu mahukuntan Nijeriya ba su ɗauko hanyar fitar da ingantattun tsare-tsaren tattalin arziki da za su taimaki talakawan ƙasar ba.
A cewarsa, abin takaici ne yadda talakawan ƙasashe masu tarin albarkatu ke fama da talauci saboda rashin mayar da hankali daga shugabanni.
Bankin ya ce duk da ci gaban da Nijeriya ta samu a sauran fannonin da ba na man fetur ba musamman a bara, amma duk da haka babu alamar samun ci gaba a ɓangaren tattalin arzikin talakawan ƙasar ta yammacin Afirka.
Rahoton ya jaddada cewa har yanzu yankin ƙasashen Sahel ne ke kan gaba a talauci a duniya gaba ɗaya, yayin da yankin ke da kaso 80 adadin mutane miliyan 695 na mutanen da ke fama da baƙin talauci.