Sa’an nan, dangane da layin dogon da wani kamfanin kasar Sin ya gina, wanda ya hada kasar Laos da kasar ta Sin, mista Siphandone ya ce, layin dogon ya haifar da alfanu sosai, a fannin tattalin arziki, wanda ya zarce yadda aka zata a baya. Kana wannan layin dogon zai zama wani bangaren sabon layin dogon da ya hada kasar Sin da kasar Singapore, wanda za a shimfida shi a nan gaba.

(Bello Wang)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: layin dogon

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Kasar Iran Ya Gabatar Da Jawabio A Taron Kolin Kungiyar ECO Musamman Kan Harin Da Kasarsa Ta Fuskanta

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Sojojin kasarsa sun koya wa ‘yan sahayoniyya masu wuce gona da iri babban darasi

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, a jawabin da ya gabatar a taron kolin kungiyar Hadin Gwiwar Tattalin Arziki ta ECO da aka gudanar a kasar Azarbaijan a yau Juma’a, ya jaddada cewa: Sojojin kasar Iran bisa doka mai lamba 51 na yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya  sun kare al’ummar Iran da mutuncin kasar da cikakken ikonta a yakin da aka yi a baya-bayan nan, kuma sun koyar da masu wuce gona da iri darasi mai girma da kuma dakile yaduwar yaki a wannan yanki.

A yayin taron koli karo na 17 na kungiyar hadin kan tattalin arziki ta ECO da aka gudanar a yammacin yau Juma’a, Pezeshkian ya yi Allah wadai da harin da gwamnatin ‘yan Sahayoniyya ta kai kan kasar Iran, yana mai cewa: Wannan gwamnatin ta fara ne da keta haddin ka’idoji da dokokin kasa da kasa da suka hada da Mataki na 2 sakin layi na 4 na Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, sannan yakin ci gaba da taimakon sojojin Amurka masu dauke da dabi’ar zalunci kan Iran.

Shugaban Iran ya kara da cewa: A cikin kwanaki 12 na hare-haren wuce gona da irin, an aiwatar da wasu munanan laifuka zalunci kan sojojin da ba sa kan aikinsu da malaman jami’a da talakawan kasa da cibiyoyin makamashin nukiliya na zaman lafiya da suke karkashin kulawar hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa, da kuma kayayyakin more rayuwa.”

Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin dimbin hasarar rayukan bil’adama da zaluncin yahudawan sahayoniyya ya janyo kan al’ummar Iran, shugaban ya ce: A bisa ka’ida ta 51 na kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya, sojojin kasar Iran sun taka rawa wajen kare halaltacciyar kasar Iran, ikon da amincin kasa, da cikakken ‘yancin kasa tare da koyar da maharan darasi mai tsauri, da kuma hana yaduwar wannan yanki a yankin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mataimakin Firaministan Sin Ya Jaddada Muhimmancin Sabbin Fasahohin Kimiyya A Fannin Aikin Gona Da Kiwon Lafiya
  • Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos
  • Shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya Na Cike Da Hangen Nesa Da Burikan Samar Da Ci Gaba In Ji Firaministan Kasar Senegal
  • Lebanon: Mutum Daya Ya Yi Shahadi A Wani Hari Na HKI
  • Sheikh Na’im Kasim Yace Kare Kasa Baya Bukatar Izini Daga Wani
  • Shugaban Kwamitin AU: Kasar Sin Aminiya Ce Da Za A Iya Dogaro Da Ita
  • Shugaban Kasar Iran Ya Gabatar Da Jawabio A Taron Kolin Kungiyar ECO Musamman Kan Harin Da Kasarsa Ta Fuskanta
  • Lardin Hainan Na Kasar Sin Ya Samu Karuwar Cinikayyar Hajoji Da Aka Daukewa Haraji Cikin Shekaru Biyar
  • Yawaitar Al’umma: Martanin Karl Marx Ga Rabaran Malthus
  • Aragchi Ya Musanta Zargin Da Jamus Take Watsawa Dangane sa Shirin Nukliyar Kasar