Aminiya:
2025-04-30@18:54:57 GMT

Janar Tsiga, Mahaifiyar Rarara da muhimman mutane da aka sace a Katsina

Published: 13th, April 2025 GMT

Yin garkuwa da mutane domin don karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a Jihar Katsina har ta kai ga ana shiga cikin manyan birane ana daukar manyan mutane ko makusantansu.

Daga manyan sojoji zuwa sarakuna da malaman addini da ’yan siyasa da attajirai da ma dalibai, babu wanda ya tsira daga wannan matsalar ta’addanci.

Gwarzon gasar Al-Kur’ani

A yayin da ake shirye-shiryen daukar azumin watan Ramadana ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da Gwarzon Gasar Al-Kur’ani na Kasa da aka kammala a Jihar Kebbi, Abdulsalami Rabi’u Fasakari a hanyarsa ta komawa gida tare da ’yan uwansa bayan Gawmna Dikko Radda ya karbi bakuncinsa tare da karrama shi.

Sai bayan makonni biyu, a yayin da ake gab da daukar azumin ne kuma danginsa suka sanar cewa sun kubuta daga hannun ’yan bindiga ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Mahaifinsa, Alaramman, Malam Rabiu Zakariya Faskari, ya bayyana cewa suna tsare a hannun ’yan bindiga a Katsina har sai da wani babban dan bindiga mai suna Yellow daga Zamfara ya zo ya karbe su da karfi,

“Muna ta addu’a har ranar Juma’a da aka zo aka ce mu fito mu tafi. Yaransa suka ɗauke mu suka kai mu wani gari, daga nan muka yi tafiyar awa huɗu kafin muka samu mota.”

Malam Rabiu, ya ce da suka hau babur sai direban ya shaida musu cewa an kashe Yellow

Sheikh Ahmed Suleiman

Irin haka ya yi kama da abin da ya faru a watan Maris na shekarar 2019 inda ’yan bindiga suka yi wa ayari malaman addinin Musulunci da ke dawowa daga taron addini daga Jihar Kebbi kwanton bauna a yankin Sheme da ke Jihar Katsina, inda suka yi garkuwa da fitaccen makarancin Al-Kur’ani nan, Sheikh Ahmed Muhammad Sulaiman, da wasu malamai hudu. Sai da malaman suka shafe kwanaki 12 cur a hannun ’yan ta’addan kafin su sako su.

Janar Maharazu Tsiga

Idan ba a manta ba, kafin sace su Alaramma Abdulsalamu ne ’yan bindiga suka kutsa gidan LaftanarJanar Maharazu Tsiga (ritaya) tsohon Shugaban Hukumar Kula da Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC) da karfin tuwo suka yi awon gaba da shi, sai da ya shafe sama da kwanaki hamsin a hannunsu kafin a sake shi tare da sauran mutane 18 da aka sace su tare a mahaifarsa da ke Tsiga a Jihar Katsina.

Ko a karshen makon da ya gabata, sai da ’yan bindiga suka yi garkuwa da kusan mutum 60, yawancinsu mata da kananan yara a kauyukan kananan hukumomin Dandume da Funtua, inda suka kashe wasu mutum shida.

Yayan Gwamna Dikko Radda

Wani daga cikin manyan mutane da aka yi garkuwa da shi da aka yi a baya-bayan nan ta girgiza Jihar Katsina shi ne, yayan Gwamna Umaru Dikko Radda wanda kuma shi ne Maigarin Radda, Alhaji Kabir Umar Radda, sai da aka biya kudin fansa kafin a karbo shi daga hannun ’yan bindiga.

A duk lokacin da Gwamna Radda zai yi magana a kan batun tsaro ya kan kawo misali da abin da ya faru ga wannan dan uwa nasa.

Surukar tsohon Gwamna Masari

Kwatsam sai aka ji labarin an sace sararkuwar tsohon gwamna Masari Hajiya Hauwa a lokacin kuma yana kan mulki.

Satar dattijuwar ta bayar da mamaki domin kuwa a yayin da ake zargin barayin daji ne suka sace ta, sai aka gano cewa wasu matasa ne karkashin wani da ake yi wa lakabi da Yalo suka dauke ta a gidanta da ke can wajen sabon titin Kwado a garin Katsina suka hannanta ta ga wasu Fulani da ake zargi da satar shanu da aikata kisan haka-kawa da kuma garkuwa da mutane.

Daga bisani dai an yi nasarar karbo ta, daga bisani aka kama matasan da suka sace ta da farko. Nan ma an samu bayanai masu karo da juna inda wasu ke cewa sai da aka biya kudin fansa, wasu kuma na cewa lallashi ne ya sa aka sako ta.

Duk wadannan abubuwa sun faru ne bayan gwamnatin Masari ta nemi sasanci da wadannan ’yan bindigar.

Magajin Garin Daura

A cikin watan azumin shekarar 2022 ne kuma aka wayi gari da labarin sace Magajin garin Daura, Alhaji Musa Umar, wanda suruki ne ga hadimin Shugaban Kasa Buhari.

Wasu mutane ne a cikin mota suka zo suka yi awon gaba da wannan basarake, kamar kamar dai yadda aka sace surukar Masari.

Buhari dan asalin garin Daura ne kuma can yake zuwa hutun sallah, kuma abin ya faru ne a ’yan makonni kafin ya tafi hutun sallah a masarautar ta Daura.

Sai dai hukumomi sun ce babu ko sisin da aka biya wajen kubutar da shi domin Rundurar ’Yan Sanda masu Yaki da Ayyukan Ta’addanci karkashi jagorancin Abba Kyari ne suka ceto shi a garin Kano a gidan da aka tsare shi tare da kama masu garkuwar.

Hakimai da Dagattai

Hatta da masu gari ba su tsira ba, sai dai wasu sukan samu kubuta ko nan take ko kuma a ana tafiya da su kafin a kai su maboyar ’yan ta’addan.

Amma a lokacin da barayin daji suka je za su yi garkuwa da Hakimin ’Yantumaki, Marigayi Alhaji Abubakar Attiku Maidabino, ya ki yarda ya ba da kai bori ya hau, nan take suka bude masa wuta a cikin dakin da ya buya, suka kashe shi.

Sai kuma Maigarin Wurma, wanda kamar yadda muka samu labari, ba a fita da shi daga cikin garin ba wani daga cikin barayin ya nuna mashi wani zaure ya ce, ya shige ciki.

Dan uwan Dahiru Mangal

Kazalika, akwai wani da ke matsayin da ga hamshakin dan kasuwar nan Alhaji Dahiru Mangal wanda ake zargin dangantakarsa da attajirin tasa masu garkuwar suka dauke shi.

Mahaifiyar mai Gidajen Man Shema

Hakazalika ’yan bindaiga sun yi garkuwa da mahaifiyar wani dan kasuwar da ke garin Dutsinma, mai suna Alhaji Mamman Nagogo wanda shi ke da gidajen man Shema.

Ita ma wannan dattijiuwa sai da danginta suka biya kudin fansa kafin ta shaki iskar ’yanci daga hannun bata-garin.

Mahaifiyar Rarara

Shi ma fitaccen mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara mahaifiyarsa ta shiga hannun masu garkuwa da mutane, inda ta shafe kwanaki da dama kafin jami’an tsaro su kubutar da ita.

Shugaban NURTW

Shugaban Kungiyar Direbobi ta Kasa (NURTW) reshen Jihar Katsina Alhaji Musa Garba ’Yandoma shi ma ya shiga hannun masu garkuwar kafin daga bisani a kubutar da shi.

Daliban Kankara

Sace daliban a Makarantar Sakandaren Kankara na daya daga cikin garkuwa da mutanen da zai yi wuya a manta da su, kasancewar a lokacin shi ne irinsa na farko da aka yi a Jihar Katsina, mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Kasurgumin dan bindiga Auwalun Daudawa wanda shi ma ya bakunci lahira ne ya jagoranci sace daliban a shekarar 2021 ya rarraba yaran zuwa wurare ciki kuwa har da yankin Karamar Hukumar Danmusa mai makwabtaka da Kankara, ya tsere da mafi yawansu zuwa dajin Zamfara.

Sai da aka kai ruwa rana tare da samun rahotanni masu karo da juna kafin fitowar yara, domin kwa har kungiyar Boko Haram sai da ta yi ikirarin ita ke da alhakin sace su.

A waje guda kuma, gwamnatin jihar ta yi ikirarin cewa ba ta biya kudin fansarsu ba, amma ta samu hadin kai da taimakon gwamnatin Jihar Zamfara a karkashin jagorancin Gwamna Bello Mohammed Mutawalle da sojojin Nijeriya, wadanda daga bisani suka ceto su.

Amma wasu rahoton sun ce sai da aka biya milyoyin kudin da masu garkuwar suka nema kafin sako ayran.

Shi kansa Auwalun Daudawa a wata hira da Jaridar Aminiya ta yi da shi, ya bayyana cewa sai da aka ba shi kudin fansa, amma dai ba su kai yawan abin da ya nema ba.

Kisan gillar ’yan bindiga

Sa’anan akwai wasu manyan hare-hare biyu da ’yan ta’addar suka kai a wasu yankunan jihar wadanda har gobe ake tunawa da su. Na farko shi ne, wanda Adamu Aleru, dan bindigar nan da ’yan sanda suka sanya tukuicin wasu miliyoyin kudi ga duk wanda ya yi sanadin kamo shi, ya jagoranci yaransa a kan babura kimanin 150 suka kai a garin Kadisau na Karamar Hukumar Faskari.

A wannan harin kusan kowane babur dauke yake da mutane uku kowannesu da bindiga, kamar yadda wani wanda aka kai harin da shi ya shaida wa manema labarai a hedikwatar ’yan sanda bayan an kama shi a wancan lokacin, a shekarar 2020.

Ya bayyana cewa dalilin kai harin shi ne, saboda jami’an tsaro sun kama dan Alerun a wani harin da suka kai.

Hari na biyu shi ne, wanda aka kai a garin Tsauwa inda ’yan bindigar suka kone daukacin garin sai da duk abin da ke cikinsa (mutum ko dabba) ya zama gawayi, in banda ’yan kalilan da suka tsallake rijiya da baya.

A harin ne aka tsinci gawar mace da ciki amma ta zama gawayi, wata kuma da goyo ta lullube wasu yaran, amma dukkansu sun kone kurmus sun zama gawayi, lamarin da ya sa jami’an tsaro da ’yan jarida zubar da hawaye.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: daliban kankara garkuwa da mutane Jihar Katsina Maharazu Tsiga garkuwa da mutane yan bindiga suka biya kudin fansa a Jihar Katsina yi garkuwa da masu garkuwar masu garkuwa da aka biya

এছাড়াও পড়ুন:

Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji kuskure ne — Janar Chibuisi

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa kuskure ne abin da jami’anta ke yi na cin zarafi da cin zalin fararen hula saboda sun sanya kayan sojoji.

Shugaban Sashen Hulɗar Sojoji da Fararen Hula na rundunar, Manjo-Janar Gold Chibuisi, bayyana cewa rundunar tana hukunta duk jami’inta da aka kama da laifin cin zalin farar hula saboda sanya kayan sojoji.

Ya ce duk da haka doka ta haramta wa fararen hula sanya kayan sojoji ba bisa ka’ida ba, kuma laifi ne da zai iya kai su gidan yarin.

Manjo-Janar Gold Chibuisi, ya ci gaba da cewa doka ba ta ba ta ba sojoji ikon hukuntawa balantana cin zalin masu aikata hakan ba. Sai kuma ta ba su ikon kama masu sojan gona da kayansu, kuma an ba sojoji horo a kan kama masu aikata hakam, su miƙa shi ga ’yan sanda domin gurfanarwa a gaban ƙuliya.

Aminu Bayero ya naɗa Sanusi a matsayin Galadiman Kano NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”

“Duk waɗannan abubuwan — na cin zalin da cin zarafin da sojoji ke yi wa masa sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba — ba daidai ba ne. Muna kuma wayar da kansu a game da hakan, sa’annan duk sojan muka samu hujja a kansa kuma, muka yi masa hukunci mai tsanani,” in ji shi.

‘Sanya kaya soja haramcin ne ga fararen hula’

Sai dai kuma Manjo-Janar Gold Chibuisi ya yi gargadi ’yan Najeriya su guji sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa mutunta kayan sojo wani muhimmin sashi ne na ƙarfafa tsaron ƙasa.

Ya jaddada cewa yin amfani da kayan aikin soja ba bisa ƙa’ida ba ga mutanen da ba su da izini ya saɓa wa doka kuma yana taimakawa ayyukan laifi, yana mai cewa bin irin wannan shawarar zai samar da yarda tsakanin sojoji da jama’a.

Ya yi wannan gargaɗin ne a Abuja a ƙarshen mako a wani taron tattaunawa da ’yan jarida, inda ya ce, “Sanya kayan sojoji ga mutumin da ba soja ba ya saɓa wa dokar ƙasa. Idan kai ba soja ba ne ko jami’in tsaro, yin amfani da unifom ɗinsu — ko kana son sa ko ba ka so — laifi ne.”

Chibuisi ya jaddada cewa dole ne a mutunta doka don kiyaye mutunci da tsaron rundunonin soji, yana mai gargadin cewa masu aikata laifin na iya fuskantar ɗauri a kurkuku.

“Idan kuna son aikin soja, ku shiga aikin soja. Kada ku saka kayanmu idan ba a cikinmu kuke ba,” in ji shi.

Game da haɗarin tsaro da ake tattare da sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba, Chibuisi ya bayyana cewa masu aikata laifuka na ƙara amfani da kakin soja don aikata laifuka, wanda ya sa ya zama da wahala ga fararen hula da hukumomin tsaro su gane sojojin gaske da na bogi.

Ya ce, “A halin yanzu, akwai ’yan fashi da yawa da ke amfani da kayan soji don aikata laifuka. Idan mutane suka ci gaba da yin ado da kayan sojoji, ta yaya za ku bambance tsakanin ɗan fashi da sojan gaske?”

Ya yi kira ga iyalai da al’ummomi da su taimaka wajen wayar da kan jama’a daga matakin gida.

“Idan wani da kuka sani ba ne ya fito sanye da ku ce masa, ‘Dakata, yau ka shiga aikin soja, cire wannan abin mana.’ Ka guji a kama ba.”

Janar din ya ci gaba da bayanin cewa an horar da sojoji don kama fararen hula da aka samu sanye da kayan soja kuma a miƙa su ga ’yan sanda don gurfanar da su a gaban kotu.

Ya kuma jaddada mahimmancin hana aikata laifin kafin ya faru: “Wani gefen shi ne sojojinmu su yi abin da ya dace idan sun ga haka, ɗayan gefen kuma shi ne fararen hula kada su yi hakan kwata-kwata.”

Yayin da yake bayyana bambanci tsakanin Najeriya da sauran ƙasashe a kan wanna batu, Manjo-Janar Chibuisi ya ƙara da cewa, “Nan ba Amurka ba ce. Ba za ku ce saboda fararen hula na sanya kayan sojoji a Amurka, a nan ma dole ya kasance haka. Ƙari ga haka, ƙalubalen da muke fuskanta a nan, ba na tunanin suna da su a Amurka.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu zai ziyarci Katsina
  • Sojoji Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga , Sun Ceto Fasinjoji 6 A Taraba
  • ‘Yansanda Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane 12 Da Masu Sayar da Makamai 3 A Taraba Da Kaduna
  • Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok
  • Sojoji Sun Ceto Mutum 50 Da Aka Sace, Sun Ƙwato Shanu 32 A Katsina
  • Bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 26 a Borno
  • Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi
  • Ma’aikata 240 na karɓar albashi biyu, wasu 217 na amfani da lambar BVN ɗaya a Kano
  • Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji kuskure ne — Janar Chibuisi
  • Uganda Ta Sanar Da Kawo Karshen Ebola Da Ta Barke A Kasar