Wani mutum wanda yake nuna kin amincewa da zaluncin da HKI yake yi wa mutanen Gaza, ya hau kan hausumiyar agogon “ Big-Bang”   a birnin London dauke da tutar Falasdinu.

An sami cunkuson motoci a yankin Westminster dake birnin London a jiya Asabar,yayin da masu ceto suke kokarin isa ga mutumin domin sauko da shi daga kan hausmiyar agogon.

Jami’an ‘yan sandan sun sanar da samin rahoton abinda ya faru da misalin karfe 7 na safe,kuma sun fara aiki domin ganin an sauko da mutumin cikin lafiya.

Jami’an tsaro sun sanar da cewa an rufe hanyar da take zuwa majalisar saboda abinda ya faru. Haka nan kuma gadar da take zuwa Wesminster  da sauran hanyoyin da suke yankin duk an rufe su.

A kasan hasumiyar wasu mutane sun taru suna bayar da taken nuna goyon baya ga ‘yancin Falasdinu.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos

 

Ya ce, masu garkuwa da mutanen sun afka gidansa ne a daren Lahadi a lokacin da mazauna gidan ke shirin kwanciya barci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ma’aikatar Shari’ar Iran Ta Sanar Da Rataye Dan Leken Asirin Hukumar Mossad Ta Isra’ila
  • ‘Yansanda Sun Kama ‘Yan Ƙungiyar Asiri Da Ɓarayin Kifi A Jihar Neja
  • An Yi Garkuwa Da Wani Mai Hidimar Ƙasa Da Ɗalibi A Jos
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • DSS ta maka Sowore da Facebook a Kotu kan cin zarafin Tinubu
  • ’Yan sanda sun kama mutum 6 kan satar zinarin N109m a Kebbi
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
  • An Karrama Farfesa Adamu Gwarzo Kan Gudummawarsa Ga Bunƙasa Ilimin Jami’a A Nijeriya
  • Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250  a Jami’ar Ilorin