Gobara ta ƙone sashen wani asibiti a Legas
Published: 1st, March 2025 GMT
Wata gobara da ta tashi cikin ta lalata wani ɓangare na Asibitin Ago da ke kan titin Ago Palace, Okota, a Jihar Legas.
Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 8:30 na daren ranar Juma’a, inda ta shafi wani sashe na ginin mai bene hawa ɗaya, inda asibitin yake.
Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250Likitoci da marasa lafiya da ke cikin asibitin sun tsere domin tsira da rayukansu yayin da wutar ta bazu.
Babban Sakataren Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Lagos (LASEMA), Dokta Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce jami’ansu sun isa wajen gobarar da misalin ƙarfe 8:45 na dare.
Binciken da LASEMA ta gudanar ya nuna cewa gobarar ta faru ne sakamakon matsalar wutar lantarki.
Rahotanni sun nuna cewar babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata.
Jami’an kashe gobara daga LASEMA da LRU da sauran masu bayar da agajin gaggawa sun haɗa kai don shawo kan gobarar tare da hana ta bazuwa zuwa wasu gine-gine da ke kusa da asibitin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara
এছাড়াও পড়ুন:
PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu da ke da alaƙa da Wike
Rikici a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, na ƙara ƙamari, bayan da jam’iyyar ta dakatar da sakatarenta na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu da ake ganin ’yan tsagin Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike ne.
Mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Debo Ologunagba ne, ya sanar da dakatarwar bayan wani taro da Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC), ya gudanar a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
Zargin Kisan Kiristoci: Maganar Trump a kan Najeriya tsagwaron ƙarya ce — Shehu Sani Zaɓen Tanzania: Shugaba Samia ta yi tazarce da kashi 97 an ƙuri’uSauran da aka dakatar sun haɗa da Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a, Kamaldeen Ajibade (SAN); Sakataren Tsara Harkokin Jam’iyya, Umar Bature; da Mataimakin Mai Bai wa jam’iyyar Shawara kan Harkokin Shari’a.
Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda aka dakatar ba sa halartar tarukan jam’iyyar.
An dakatar da su na tsawon wata ɗaya, sannan aka miƙa lamarinsu ga Kwamitin Ladabtarwa na jam’iyyar PDP domin gudanar da bincike.
Waɗanda aka dakatar ’yan tsagin Wike ne, kuma sun raba ƙafa a rikicin da jam’iyyar ke fuskanta tun bayan zaɓen 2023.
Idan ba a manta ba, a ranar Juma’a ne, wata Babbar Kotu a Babban Birnin Tarayya, ta dakatar da PDP daga shirin gudanar da babban taronta da aka tsara yi a Ibadan, Jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamba, 2025.
Sai dai jam’iyyar ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin, kuma hakan ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da taron ba.
Wasu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar sun ce rashin jituwa a PDO shi ne babban dalilin da ya sa aka kai ƙarar taron’ kotu.