DRC Ta Sa Kudi Dalar Amurka Miliyan 5 Akan Jagororin ‘Yan Tawayen M 23
Published: 9th, March 2025 GMT
Gwamnatin jamhuriyar demokradiyyar congo ta ware kudi da sun kai dalar Amurka miliyan 5 akan duk wanda ya kamo mata shugabannin kungiyar ‘yan tawaye ta M 23 da su ka hada Corneelle Nangaa, Sultani Makenga da kuma Betrand Bisimwa.
Sai dai duk da kudade masu tsokar da DRC din ta sanya akan shugabannin kungiyar su uku, abin da kamar wuya,saboda ganin yadda wannan kungiyar take ci gaba da kutsawa cikin manyan birane tana shimfida ikonta a cikinsu.
A halin yanzu biranen Goma da Bukavu da suke a gabashin wannan kasa sun shiga karkashin ikon mayakan kungiyar ta M 23.
Dubban mutane ne dai su ka rasa rayukansu yayin da wasu dubun dubata kuma su ka bar gidajensu zuwa inda za su tsira da rayukansu.
Shugaban kasar ta DRC Felix Tashisekedi ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kakaba wa kasar Rwanda takunkumi saboda yadda take goyon baya da kuma taimaka wa kungiyar M23 da take ci gaba da rike da biranen Goma da Bukavu.Da akwai sojojin Rwanda 4,000 da suke taimakawa ‘yan tawayen na M 23.
Shugaban kasar ta DRC ya zargi Rwanda da wawason albarkatun karkashin kasar da ake kiyasin cewa sun kai na biliyoyin daloli.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Majalisar Amurka ta iso Nijeriya Don Bincika Zargin Tauye Haƙƙin Addini
Majalisar Dokokin Amurka ya iso Abuja yayin da ƙasashen biyu ke ƙara matsa ƙaimi wajen tattaunawar diflomasiyya kan haɗin gwiwar tsaro da kuma zargin tauye haƙƙin addini.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba.
“Tawagar ta ƙunshi ‘yanmajalisar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” in ji Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta.
Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar.
A cewar Ribadu, tattaunawar ta mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci, tabbatar da zaman lafiyar yanki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka.