Ramadan: ’Yan sanda sun tsaurara tsaro saboda azumi a Borno
Published: 1st, March 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta sanar da ƙarin matakan tsaro yayin da al’ummar Musulmi suka shiga watan azumin Ramadan.
Haka kuma, rundunar ta taya Musulmi murnar shigowar wannan wata mai alfarma.
Gobara ta hallaka mutum 2 a sansanin ’yan gudun hijira a Borno Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin sayaKakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso, ya bayyana cewa an kammala shirin tsaurara tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a cikin watan Ramadan.
“Mun san muhimmancin wannan wata ga ’yan uwanmu Musulmi,” in ji sanarwar.
“Saboda haka, mun ƙara sintiri da samar da jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci a faɗin jihar.”
Kwamishinan ’yan sandan Borno, CP Yusufu Mohammed Lawal, ya tabbatar da cewa rundunar tana sadaukar da kai domin kare lafiyar jama’a a cikin wannan wata.
“Burinmu shi ne kowa ya samu damar gudanar da ibadarsa cikin kwanciyar hankali da tsaro,” in ji Kwamishinan.
Haka kuma, rundunar ta buƙaci jama’a da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.
“Idan kun ga wani abu, ku sanar da hukuma,” in ji ASP Daso.
Rundunar ta kuma fitar da lambobin kiran kar ta kwana domin bayar da rahoto: 08068075581 da 08023473293.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Ramadan Tsaro rundunar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Babu wanda ya tayar da bam a Abuja —Wike
Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya ce rahotannin da ya samu na nuna babu gaskiya a labarin da ake yaɗawa cewa mai ƙunar baƙin wake ne ya tada abu mai fashewa a barikin soji na Mogadishu da ke Abuja.
Wike ya bayyana hakan ne ga manema labarai, lokacin da ya kai ziyarar duba aikin titunan da za a ƙaddamar domin bikin cikar shugaba Tinubu biyu a kan karagar mulki.
Sojoji sun halaka mayakan ISWAP da dama a Borno Bashin da ake bin Najeriya zai koma tiriliyan 162Ministan ya kuma ja hankalin ’yan jarida kan yaɗa labaran da ka iya jefa firgici a zuƙatan al’umma.
Aminiya ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a shingen bincike na barikin sojin Mogadishu, kuma hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ce a ranar Talata ta ce harin ɗan ƙunar baƙin wake ne.
“Jami’an tsaro ba su ce harin ɗan ƙunar baƙin wake ba ne. Saboda haka kar ku je kuna tsorata mutane da maganganu marasa tushe. Ku dinga binciken ƙwaƙwaf kafin yaɗa labaranku. NEMA ba shugabar tsaro ba ce, ma’aikatun tsaro na wurin.
“Abin da ya faru shi ne wani ne ya je wuraren da muke fasa dutsuna. Sai ya ɗauki nakiyar da ake fasa dutse ya saka a aljihu wataƙila don bai san illar hakan ba. Shi ne ta fashe a jikinsa. Ka ga ai hakan ba yana nufin ɗan ƙunar baƙin wake ba ne,” in ji ministan.
Sai dai ya zuwa lokacin haɗa rahoton, daga rundunar soji har ta ’yan sanda, babu wacce ta ce komai kan hakan, sun dai ce suna gudanar da bincike.