Iran Za Ta Yi Nazarin Sabuwar Gayyatar Da Amurka Ta Yi Mata Na Sabuwar Tattaunawa
Published: 8th, July 2025 GMT
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa, tana nazarin sabuwar gayyatar da Amurka ta yi mana na komawa teburin tattaunawa.
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto wata majiya mai karfi tana cewa, bayan da Amurka ta kasa dakatar da Shirin kasar na makamashin Nukiliya, ta aiko ma ta da takardar gayyata domin yin zama da ita akan teburin tattaunawa.
Majiyar ma’aikatar harkokin wajen Iran ta fada wa kamfanin dillancin labrun “Mehr” cewa, Amurka ta aiko da sakwanni ta hanyar ‘yan aike na kasashe masu yawa.”
Ma’aikatar harkokin wajen ta Jamhuriyar musulunci ta Iran tana yin nazari akan hakikanin abinda Amurkan take so, da kuma yadda tattaunawar za ta kasance wacce za ta zama ta dage takunkumai, da kuma darajar uranium din da Iran za ta tace, sannan kuma da biyanta… na barnar da aka yi mata sanadiyyar kallafaffen yaki.
Tun da dari, Amurka ta yi kokarin nuna cewa Iran ce ta bukaci ayi tatttaunawar, lamarin da Jamhuriyar musulunci ta Iran ta kore.
Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran Abbas Akarci, ya sha bayyana cewa, duk wata tattaunawa idan har za a yi ta, to za ya kasance ne akan manufar kare maslahar jamhuriyar musulunci ta Iran. Batun ci gaba da tace nadarin uranium kuwa, wani abu wanda Iran ba za ta taba ja da baya a kansa ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: harkokin wajen
এছাড়াও পড়ুন:
‘Yan Sandan Jihar Neja Sun Tabbatar Da Masu Sa-kai Kan Sahihiyar Kariya.
Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta tabbatar wa al’ummar jihar a shirye ta ke ta ci gaba da kare mutuncin daidaikun mutane da kungiyoyin da suka sadaukar da kansu domin samar musu da sahihin bayanan sirri da za su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Nijar.
‘Yan sanda a jihar Neja da ma Nijeriya ƙwararru ne don haka za su ci gaba da aiki da kuma nuna basira da ƙwarewa tare da ƙa’idarta ta sirrin rashin bayyana tushen bayanansu don samun sakamako mafi girma.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Adamu Abdullahi Elleman wanda ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, ya bayyana cewa a kwanan baya ya halarci wani taron bita da hedkwatar ‘yan sanda ta shirya kan masu bada bayanai wato Informant domin kara kwarewarsa.
Sai dai Adamu Abdullahi Elleman ya danganta raguwar ayyukan aikata laifuka a Minna babban birnin jihar da sahihan bayanai da aka samu daga jama’a, goyon baya daga babban sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun da gwamnatin jihar Neja a karkashin jagorancin Gwamna Umar Bago, da sarakunan gargajiya da kuma matakin da ya dauka na cewa a mafi yawan lokuta yakan shiga sintiri a Minna, wanda DPO da kwamandojin yankin suka goyi bayansa.
A cewarsa sakamakon wannan yunkurin da aka yi da dama daga cikin miyagu da suka tsunduma cikin ayyukan ‘yan daba, an kama su, an kuma gurfanar da su a gaban kuliya, tare da daure su a matsayin misali ga wasu.
Adamu Abdullahi Elleman ya ci gaba da cewa, ya kuma gargadi Hakimai na yankin da su rika taimaka wa miyagu cewa duk wanda aka kama za a gurfanar da shi a gaban kuliya manta sabo.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja, ya kuma yabawa babbar mai shari’a ta jihar, Mai shari’a Halima Ibrahim bisa goyon bayan da ta bayar wajen ganin an samar da shari’a cikin gaggawa, tare da samun hadin kai tsakanin ‘yan sanda da sauran kungiyoyin tsaro baya ga sabon alkawari da jami’an sa da mazaje suke yi na yakar miyagun laifuka da aikata laifuka a duk lungu da sako na jihar.
Adamu Abdullahi Elleman ya kuma kara da cewa a karkashin sa a matsayinsa na sabon kwamishinan ‘yan sanda mai kula da jihar Neja, jin dadin jami’ansa da jami’an rundunarsa shi ne babban abin da ya fi ba da fifiko wajen kara musu kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyuka masu inganci.
INT Aliyu Lawal.