Falasdinawa 13 Ne Suka Yi Shahada Wasu Da Dama Suka Jikkata A Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza
Published: 8th, July 2025 GMT
Falasdinawa 13 ne suka yi shahada da suka hada da yara kanana da mata a hare-haren bama-bamai da sojojin mamayar Isra’ila suka kai kan gidaje da matsugunan Falasdinawa a Gaza
Sojojin mamayar Isra’ila sun ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza da asubahin ranar Talata, inda suka kai hare-hare kan gidajen fararen hula da matsugunan ‘yan gudun hijira.
Asibitin Al-Shifa ya sanar da shahadan Falasdinawa hudu ciki har da wani jariri, sakamakon harin da jiragen yakin sojin mamayar Isra’ila suka kai a wani gida da ke kusa da kasuwar Carrefour a unguwar Tel al-Hawa da ke kudu maso yammacin birnin Gaza. A halin da ake ciki kuma, asibitin Baptist ya sanar da shahadan Falasdinawa biyu tare da jikkata wasu sakamakon harin da aka kai a gidan Khader al-Jamasi da ke kusa da masallacin al-Ibki da ke unguwar al-Tuffah da ke gabashin birnin.
Wata majiyar lafiya a asibitin Al-Awda da ke sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat ta bayyana cewa: Hari ya jikkata wasu fararen hula a lokacin da makarantar Abu Helu al-Sharqiya da ke dauke da ‘yan gudun hijira a sansanin ‘yan gudun hijira na al-Bureij da ke tsakiyar zirin Gaza ta fuskanci hare-haren da sojojin mamayar Isra’ila ta kai kai tsaye, lamarin da ya haifar da firgici ga iyalan da suka rasa muhallansu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila yan gudun hijira
এছাড়াও পড়ুন:
Miliyoyin Yan Najeriya Ne Suka Gudanar da Tattakin Ashoora Wasu Kuma A Makarantunsu…
Miliyoyin yan Najeriya ne suka gudanar da tattakin Ashoora a birne daban daban a kasar a jiya Lahadi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran, da farko ya nakalto daruwan da suka fito tattakin na Ashoora a Abuja babban birnin kasar a safiyar jiya Lahadi.
A wannan karon dai masu tattakin Ashoora a Abuja sun fito ba tare da sanya bakaken kaya ba saboda kaucewa rikici da kuma kamu daga Jami’an tsaro a birnin, kamar yadda suka sabayi a shekarun da suka gabata.
Labarin ya kara da cewa an gudanar da irin wannan tattakin na Ashoora a garurwa kimai 25 a duk fadin kasar, kuma an kammala ba tare da wata matsala ba.
An gudanar da tattaki a jihar Bauchi da kuma Jihar Yobe, wasu masu makokin Ashoora sun gudanar da su ne a cikin makarantu ko kuma masallatansu ko kuma wasu wurare da da suka kebe don haka Kungiyar muassasar Rasulul Azam sun gudanar da taron a makaransu da ke dan bare a birnin kano da kuma wasu wurare.