Amurka Ta Soke Dokar Da Ta Tabbatar Da Hai’at Tarirusham Cikin Jerin Kungiyoyin Yan Ta’adda
Published: 8th, July 2025 GMT
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu a takardan doka ta soke kungiyar yan ta’adda ta Jihatun Nusra, wacce ake kira Hay’at Tahrirusham a matsayin kungiyar yan ta’adda a duniya.
Shafin yanar gizo na labarai Arab News na kasar Saudiya, ya bayyana cewa shugaban ya cire HTSH daga jerin kungiyoyin yan ta’adda ne, saboda taimakawa kungiyar tabbatar da ikonta a kan kasar Siriya ta kuma share fagen dauke wa kasar takunkujman tattalin arzikin da aka dorawa kasar.
Labarin ya kara da cewa sakataren harkokin wajen kasar Amurka Marco Rubio ne ya sanya hannu a kan takardan cire shugaban kasar Siriya mai ci Ahmed Al-Sharaa ko wanda aka fi sani da Jolani daga jerin yan ta’adda a duniya. Wanda kuma zai share fagen wa ma’aikatar kudin Amurka ta kara virewa kasar Siriya takunkuman tattalin arziki da aka dorawa a kasar ta Siriya.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: yan ta adda
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.
A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp