Kakakin dakarun rundunar Izzudden-Qassam ya bayyan cewa: ‘Yan gwagwarmaya sun tarwatsa wani mutum-mutumi da sojojin mamayar Isra’ila suka makare da harsashai dauke da makami mai linzami a lokacin da ake shirya shi

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kakakin rundunar sojin Qassam bangaren sojin kungiyar Hamas Abu Obeida, ya yi bayyana cewa: ‘yan gwagwarmaya sun nuna jarumtaka wajen tunkarar makircin ‘yan mamaya mai sarkakiya a gwagwarmayar Beit Hanoun, inda suka kara raunana martabar sojojin mamaya tare da rusa makircinsu.

.

Kakakin rundunar sojin Qassam Abu Obeida, ya kara da cewa: Hadadden aikin na Beit Hanoun wani karin mataki ne da ‘yan gwagawarmaya suka dauka na raunana makiya tare da rusa martabar sojojin mamayar Isra’ila.  

Yana mai jaddadad cewa: Yakin da ‘yan gwagwarmaya ke yi da makiya daga arewacin Zirin Gaza zuwa kudancinta, zai kara haifar da hasara ga ‘yan mamaya a kowace rana, kuma ko da kuwa a ‘yan kwanakin nan sun samu nasarar kubutar da dakarunsu gwagwarmaya daga wani makircin ‘yan mamaya tare da killace sojojin mamayar Isra’ila da haka ya Sanya suka kara kama fursunonin yaki.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: sojojin mamaya

এছাড়াও পড়ুন:

 Maduro Ya Jinjina Wa Jagororin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran

Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro wanda ya bude bikin baje kolin littatafai na kasa da kasa a kasarsa, ya yi jinjina ga Imam Khumaini  ( r.a) da kuma jagoran juyi Ayatullah Sayyid Ali Khamnei.

Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto cewa, A yayin bikin bude taron baje kolin, shugaban kasar na Venezuela ya bayyana girmamawar da yake yi wa jagoran juyin musulunci, tare da yin ishara da ganawarsu a shekarun 2000 da 2010.

Haka nan kuma shugaban kasar ta venezuella ya bayyana yadda ya ga al’adu da ci gaban al’ummar Iran da su ka ja hankalinsa da burge shi matuka.

Bugu da kari shugaba Maduro ya bayyana zurfin hikimar da ya gani a tare da jagoran juyin musulunci,  da kuma yadda yake kare tsarin jamhuriyar musulunci da ci gaba da wanzuwarsa a cikin nutsuwa, hakuri, juriya da kuma tsayin daka.

Har ila yau, shugaba Maduro ya yi ishara da yadda Iran take cika alkawalinta a fagen kawancenta da kasarsa Venezuela.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kakakin Hafsan Hafsoshin Sojin Iran Ya Ce: Iranta Dorawa Amurka Alhakin Duk Harin Da Ta Fuskanta
  • ‘Yan Gwagwarmayar Falasdinu Sun Halaka Sojojin Mamaya Biyar Tare Da Jikkata Wasu Goma Na Daban
  • Falasdinawa 13 Ne Suka Yi Shahada Wasu Da Dama Suka Jikkata A Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila A Gaza
  • Sin Na Bikin Cika Shekaru 88 Da Dukkan Al’ummar Kasar Ta Fara Yakin Kin Jinin Harin Sojojin Japan
  • Sojoji Sun Fatattaki Ƴan Bindigar Da Suka Zo Sace Wani Ɗan China
  • Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Kai Hare-Haren Wuce Gona Da Iri Kan Lardin Hodeidah Na Kasar Yemen
  • Kungiyoyin Gwagwarmayar Falasdinawa Sun Yi Allah Wadai Da Harin Mamayar Isra’ila Kan Kasar Yemen
  • Babban Mufti Na Masarautar Oman Ya Yi Kakkausar Suka Kan Masu Son Kulla Alaka Da H.K.Isra’ila
  •  Maduro Ya Jinjina Wa Jagororin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran