Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa; Amurkawa sun jefa bama-bamai a kan teburin tattaunawa tare da lalata harkar diflomasiyya

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce Iran na gudanar da shawarwari ba na kai tsaye ba da Amurka, amma sai suka jefa bama-bamai a kan teburin tattaunawa tare da lalata hanyar diflomasiyya.

A wata hira da Tucker Carlson mai watsa labarai na Amurka, shugaba Pezeshkian yayi magana da Carlson cewa: Mr. Carlson! Mun kasance a kan teburin shawara kuma ana cikin tattaunawa saboda shugaban Amurka ya kira zuwa ga zaman lafiya kuma a wannan taron sun gaya mana cewa gwamnatin Isra’ila ba za ta kai wani hari ba.

Pezeshkian ya kara da cewa: Amma a jajibirin taro na shida, muna cikin tattaunawa, sai suka jefa bama-bamai a kan teburin tattaunawa tare da lalata harkokin diflomasiyya.

Dangane da bincike da tantancewa, shugaban na Iran ya ce: “Ba shakka a shirye muke mu koma tattaunawa da tantancewa, ba mu taba kaucewa tantancewa ba, kuma a shirye muke mu sake gudanar da wani bincike.” Abin takaici, bayan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliya, yawancin kayan aiki da wuraren sun lalace kuma ba su da sauƙin samuwa. Dole ne mu jira mu ga ko za a iya sake samun damar nazarin shiga wani sabon tattaunawa nan gaba.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar China Ta Yi Watsi da Barazanar Trump Na Kakabawa Kasashen BRICS Karin Takunkuman Tattalin Arziki

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen China Mao Ning ta zargi kasar Amurka da nuna adawa da kungiyar BRICS ta raya tattalin arziki na kasashen kungiyar ta kuma kara da cewa kokarin kare kanta da ga shirye-shiryen BRICS ba zai amfane ta ba.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar China na cewa kungiyar kungiya ce wacce bata son babakere da Amurka take nunawa a yadda take tafiyar da al-amura a duniya kamar Ita ce, take iko da kowa.

Tace kungiyar tana son duniya ta zama mai kudubobi, wadanda su ma za’a iya fada su kuma aikata abinda suke so karkashin dokokin duniya. Don haka mamayar da takardan dalar Amurka ta yiwa mafi yawan harkokin kasuwanci a duniya bai yi masu ba. Sauran kasashen ma suna da kudade suna kuma son ganin sun fita daga danniya da babakeran da Amurka take ya a duniya.

Dole ne duniya ta zama mai kubobi, sai dai a yi aiki tare don tafiyar da al-amura a cikinta.

Kafin  haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump bayyana cewa zai kakabawa kasashen da suke cikin kungiyar BRICS takunkuman karin kodin fito na kasha 10% don kare kasar Amurka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kakakin Hafsan Hafsoshin Sojin Iran Ya Ce: Iranta Dorawa Amurka Alhakin Duk Harin Da Ta Fuskanta
  • Kasar China Ta Yi Watsi da Barazanar Trump Na Kakabawa Kasashen BRICS Karin Takunkuman Tattalin Arziki
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yace Mutanen Kasarsa Suna Cikin Shiri Don Kare Kansu Da Karfi
  • HKI Tana Tana Son Ci Gaba Da Yaki Kuma Trump Yana Tare Da Shi
  • Reuters: Amurka Tana Da Shirin Korar Falasdinawa Daga Gaza
  • Mutane 21 Suka Mutu A Hatsarin Mota A Hanyar Zaria Zuwa Kano
  • Malamin Addinin Musulunci Yayi Kira Da Ayi Gaggawa Gyaran Hanyar Zamfara
  • China Ta Maida Martani da Haka Kayakin Kiwon Lafiya Na Tarayyar Turai Shigowa Kasar
  • Shugaban Kasar Iran Ya Ce Kungiyar ECO Ta Yi Tir Da Hare-Haren HKI Kan Kasarsa