Farashin fetur na iya tashi yayin da Dangote ya daina sayar da mai a Naira
Published: 20th, March 2025 GMT
’Yan Najeriya na iya fuskantar ƙarin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kuɗin Naira.
Matatar, wacce ke siyan ɗanyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan ɗanyen mai da dalar Amurka.
Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Tinubu ya rantsar da Ibas a matsayin mai kula da RibasAn ƙirƙiro yarjejeniyar siyan ɗanyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai.
Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar ɗanyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira.
Sai dai rashin cika alƙawari daga NNPCL ya sa yarjejeniyar ta gaza ɗorewa.
Wata majiya ta bayyana cewa, “NNPCL bai cika alƙawarin da ya ɗauka ba, hakan ya sa Dangote ba shi da wani zaɓi illa ya fara siyan ɗanyen mai da dala.
“Yanzu matatun cikin gida sai sun samu dala kafin su iya ci gaba da aiki.”
Matatar Dangote ta ce, “Dole ne mu daidaita kuɗin sayar da kayayyakinmu da kuɗin da muke siyan ɗanyen mai. Yarjejeniyar Naira ba ta samar da isasshen ɗanyen mai da zai iya kula da aikinmu ba.”
Masana sun yi gargaɗiMasana tattalin arziƙi sun yi gargaɗin cewa wannan mataki zai haddasa tashin farashin man fetur yayin da aka fara samun sauƙin tashin kayan masarufi.
Dokta Thomas Ogungbangbe, wani masanin harkokin makamashi, ya ce, “Idan ana siyan ɗanyen mai da dala, dole ne a sayar da man fetur a farashin kasuwar duniya. Wannan zai ƙara matsin lamba ga dalar Amurka kuma ya jefa ’yan ƙasa cikin ƙarin wahala.”
A cewarsa wannan mataki na iya janyo ƙaruwar shigo da mai daga ƙasashen waje.
“Muna tunanin tace mai a gida zai warware matsalar tsadar mai, amma yanzu muna dawowa kan matsalar da muka nemi mu magance ta,” in ji Dokta Ogungbangbe.
Dokta Marcel Okeke, wani ƙwararre a ɓangaren harkar man fetur, ya buƙaci gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa.
“Dawo da tsarin sayen ɗanyen mai da Naira zai taimaka. Idan ba a yi hakan ba, farashin man fetur zai ƙara hauhawa, wanda zai haddasa tashin gwauron zabin hauhawar farashi kayayyaki da kuma matsi ga tattalin arziƙi,” in ji shi.
Sakamakon tashin farashin canjin dalar Amurka, wasu masana sun yi hasashen cewa farashin man fetur na iya haura Naira 1,000 kan kowace lita a makwanni masu zuwa, idan ba a ɗauki matakin shawo kan lamarin ba.
Ƙungiyoyin ƙwadago sun ja dagaDangane da wannan lamari, ƙungiyoyin ƙwadago da na kare haƙƙin masu amfani da kayayyaki sun fara shirye-shiryen gudanar da zanga-zanga kan yiwuwar ƙarin farashin mai.
Ƙungiyoyin Ƙwadago na Najeriya na NLC da TUC, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakin gaggawa domin daƙile lamarin da ka iya jefa al’umma cikin wahala.
“Wannan mataki da Matatar Dangote ta ɗauka zai sanya rayuwa ta ƙara tsananta ga miliyoyin ‘yan Najeriya da suka riga suka faɗa cikin matsin tattalin arziƙi,” in ji Shugaban NLC, Joe Ajaero.
Farashin kuɗin sufuri na iya tashiA halin yanzu, ana sa ran hauhawar farashin man fetur zai ƙara tsadar kuɗin sufuri, wanda hakan zai daɗa ta’azzara wahalar rayuwa.
Wasu direbobin mota sun nuna damuwarsu cewa idan farashin mai ya ƙaru, dole ne su ƙara kuɗin abun hawa, wanda zai ƙara dagula halin da talakawan Najeriya ke ciki wajen yin zirga-zirga a kullum.
Idan ba a samu mafita cikin gaggawa ba, tasirin lamarin zai iya shafar tattalin arziƙin Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dalar Amurka ɗanyen mai Naira Tashin Farashi yarjejeniya siyan ɗanyen mai da farashin man fetur
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Jami’ai Da ‘Yan Kasuwar Ta Tunusiya Ta Gana Da Mataimakin Shugaban kasar Iran
Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran
A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki kwararan matakai wajen fadada dangantakar tattalin arziki tsakanin Iran da Tunusiya.
A yayin taron, wanda aka gudanar a ofishinsa tare da halartar jakadan kasar Tunisiya a Iran Imed Rahmouni da tawagar da ke tare da shi, Aref ya bayyana cewa, dangantakar siyasa da ke tsakanin al’ummar Iran da Tunisiya na tafiya cikin wani yanayi mai ma’ana, amma hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya ya kasance kasa da abin da ake bukata, bisa la’akari da dama da karfin da bangarorin biyu ke da shi.
A yayin ganawar, Aref ya tunatar da ziyarar da ya kai birnin Qairawan na kasar Tunusiya shekaru ashirin da suka gabata, lokacin da ya rike mukamin mataimakin shugaban kasar na farko na Jamhuriyar. Ya kara da cewa a lokacin yana jin kamar ya ratsa daya daga cikin garuruwan Khorasan na kasar Iran, yana daukar birnin Qairawan wata alama ce ta hadin kan al’ummar musulmi da alakar al’adu da addini tsakanin Iran da Tunisiya.