Cikar NUJ Shekaru 70: ‘Yan Jarida Abokan Hulɗa Ne Wajen Aza Kyakkyawar Makoma – Gwamnan Gombe
Published: 20th, March 2025 GMT
Ya kuma nuna jin daɗinsa da irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Alhassan Yahayan, inda ya ce an ɗora ƙungiyar kan kyakkyawan turbar da ya kamata don ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunƙasa aikin jarida a Nijeriya.
Yahaya ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin Jihar Gombe da ‘yan jarida, yana mai bada tabbacin cewa wannan kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa za su kasance ginshiƙin gudanar da mulki a jihar.
“Mu a Jihar Gombe muna alfahari da daɗaɗɗiyar dangantakar da muka ƙulla da ‘yan jarida; ‘yan jarida abokan aikinmu ne masu ƙima a fagen kawo ci gaba, kuma muna ci gaba da jajircewa wajen ganin sun ci gaba da yin aiki a yanayin da zai bunƙasa sana’o’insu da ‘yancinsu,” inji Gwamna Inuwa Yahaya.
Ya kuma bada tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa gwiwa da NUJ da sauran ƙungiyoyin yaɗa labarai don ba su damar ci gaba da kuma gudanar da muhimmiyar rawar da suke takawa wajen ankarar da gwamnati da wayar da kan jama’a.
Gwamna Inuwa ya ƙara da cewa, “Gudunmawar da kuka bayar na da matuƙar muhimmanci wajen inganta demokraɗiyya, da riƙon amana, da kuma shugabanci na gari a Nijeriya, muna godiya da irin rawar da kuke takawa wajen faɗakar da jama’a, da kare gaskiya, da kuma inganta manufofin gaskiya da adalci,” in ji Gwamna Inuwa Yahaya.
Ya kuma jaddada ƙudurin gwamnatin jihar na yin haɗin gwiwa mai ɗorewa da ‘yan jarida, inda ya jaddada muhimmancinsu wajen ci gaban Jihar Gombe dama Nijeriya baki ɗaya.
“Muna fatan ƙara ƙarfafa haɗin gwiwarmu da NUJ, kuma muna da yaƙinin cewa, tare, za mu ci gaba da gina ƙasa mai wadata, zaman lafiya da ci gaba,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Jigawa ta Kare Kasafin Kudinta a Gaban Majalisa
Daga Usman Muhammad Zaria
Ma’aikatar mata da walwalar jama’a ta jihar Jigawa za ta kashe naira milyan dubu 10 da milyan 599 wajen gudanar da manyan ayyuka da harkokin yau da kullum a sabuwar shekara.
Kwamishinar ma’aikatar, Hajiya Hadiza Abdulwahab, ta bayyana hakan lokacin kare kiyasin kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamatin harkokin mata na majalisar dokokin jihar Jigawa.
A cewar ta, za su mayar da hankali wajen inganta shirye shiryen bunkasa rayuwar mata da al’amuran da su ka jibinci kananan yara domin bada kariya ga masu rauni a cikin al’umma.
Hajiya Hadiza Abdulwahab ta ce ma’aikatar ta samu nasarori wajen aiwatar da tanade tanaden kasafin kudin 2025, yayin da za su ci gaba da daukar matakan da su ka dace domin inganta ayyukan su a sabuwar shekara.
Ta kuma yi nuni da cewar, batun kula da rayuwar masu rauni a cikin al’umma ya kasance ginshiki daga cikin kudurorin Gwamna Malam Umar Namadi.
Hajiya Hadiza, ta bada tabbacin aiki tukuri domin samun nasarar da ake bukata a sabuwar shekara.