Dakarun Sashe na 2 tare da hadin gwiwar sojojin sama na rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto mutane 101 da aka yi garkuwa da su a fadin Kankara a jihar Katsina da Shinkafi a jihar Zamfara a ranakun 17 da 18 ga watan Maris 2025.

 

A cewar sanarwar mai Magana da aywun rundunar Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubukar Abdullahi ya bayyana cewa, a yayin farmakin an kashe ‘yan ta’adda 10 a wata arangama da suka yi a gundumar Faru da ke karamar hukumar Maradun.

 

Ta ce an fara kai farmakin ne a jihar Katsina, inda sojoji suka kai farmakin a kan ‘yan ta’addan a babbar filin Pauwa da ke karamar hukumar Kankara.

 

“Hakan ya yi sanadin kashe ‘yan ta’adda 3 tare da ceto mutane 84 da aka yi garkuwa da su.

 

A halin da ake ciki kuma, a jihar Zamfara, sojojin sun aiwatar da wasu ayyuka a yankin Bagabuzu da ke gundumar Faru, cikin karamar hukumar Maradun wanda ya kai ga halaka ‘yan ta’adda 7 tare da kwato babur da dai sauransu.

 

Bugu da kari, an yi nasarar ceto mutane 17 da wani sarkin ‘yan ta’adda ya yi garkuwa da su daga kauyukan Tsibiri da Doka da ke karamar hukumar Shinkafi, kuma a halin yanzu suna samun kulawar likitoci a wani asibiti da ke yankin.

 

Sanarwar ta bayyana cewa, Operation Fansan Yamma na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da tsaron al’ummar jihohin Katsina da Zamfara.

 

REL/AMINU DALHATU

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Fansar Yamma Zamfara karamar hukumar yan ta adda

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC

Karin bayani na tafe

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Yaba Ma Iyaye Bisa Goyon Bayansu ga Shirin Rigakafin Shan Inna a Karamar Hukumar Ringim
  • Za a Yi wa Yara 194,000 Rigakafin Cutar Shan Inna a Karamar Hukumar Birnin Kudu
  • Gwamnan Jihar Ribas ya sauya sheka zuwa APC
  • An dakatar da Shugaban Karamar Hukumar Lafia
  • Pakistan ta Bai Wa Taliban Ta Aghanistan  Zabi A Tsakanin Mu’amala Da Ita Ko  Da  ‘Yan Ta’adda
  • Zaben 2027: NNPP Ta Sha Alwashin Maye Gurbin Tinubu da Radda
  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato
  • Rashin Tsaro: Gwamnatin Tarayya ta gaza — Kwankwaso
  • Mutum 5 sun rasu sanadin gobara da faɗa wa rijiya a Kano
  • Amurka: Mun Yi Kokarin Kifar Da Gwamnatin JMI Har Sau Biyu Ba Tare Da Samun Nasara Ba