Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Yace Mutanen Kasarsa Suna Cikin Shiri Don Kare Kansu Da Karfi
Published: 8th, July 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Aran Abbas arachi ya bayyana cewa mutanen kasarsa a shirin suke su ci gaba da kare kasarsu daga Amurka da kuma HKI .
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Abbas Aragchi yana fadar haka a jiya litinin a lokacinda yake ganawa da tawagar kasar Brazil a gefen taron kungiyar BRICS karo 17 wanda ke tafiya a halin yanzu a birnin Rio de Jenero na kasar Brazil.
An gudanar da wannan taron ne saboda hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa JMI a baya bayan nan, da kuma tasirinsa a cikin al-amuran siyasa da kuma tattalin arziki a yankin Asiya ta yamma da kuma duniya gaba daya.
Abbas Aragchi ya bayyana cewa hare-haren HKI da kuma Amurka ya sabawa dikokin kasa da kasa sannan ko wane bangare yana da rawar da zai take don ganin an tabbatar da zaman lafiya a duniya.
A nashi bangaren ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov yace: hare-hare kan kasar Iran musamman a kan shirinta na makamashin nukliya na zaman lafiya abin yin tir da shi ne. Sannan ya kara da cewa kasar Rasha a shirye take ta taimaka ko a fagen kwamitin tsaro na MDD ne.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sarkin Musulmi ya buƙaci gwamnonin Arewa suke saurarar ƙorafin jama’a
Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar III, ya shawarci gwamnonin jihohin Arewa 19 su riƙa sauraron masu sukarsu tare da amfani da shawarwarin da ake ba su domin inganta salon mulkinsu.
Ya bayar da wannan shawara ne a ranar Litinin, yayin taron haɗin gwiwar Gwamnonin Arewa da Sarakunan Gargajiya a Kaduna.
’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 13 da ɓacewarsu a Borno ’Yan bindiga sun sace fasto da matarsa masu ibada a KogiSarkin Musulmi, ya ce bai kamata shugabanni su yi biris da ƙorafin jama’a ba, musamman a wannan lokaci da Arewa ke fama da matsalolin rashin tsaro, talauci da matsin tattalin arziƙi.
A cewarsa, babu wani gwamna ko shugaban ƙasa da zai nemi ƙuri’un jama’a sannan bayan ya hau mulki ya juya musu baya.
Ya nuna damuwa cewa mutane da dama na zargin gwamnonin da rashin yin aiki, alhali suna fuskantar matsin lamba.
Sarkin ya shawarce su da su rika karɓar ƙorafe-ƙorafe masu amfani tare da gyara inda ya dace, domin hakan na taimakawa wajen yanke shawara mai kyau.
Haka kuma, ya yi kira da a ƙara samun haɗin kai a tsakanin gwamnonin, inda ya ce hakan ne zai taimaka wajen inganta Arewa da daidaita ƙasa baki ɗaya.
Sarkin Musulmi ya tabbatar wa gwamnonin cewa sarakunan gargajiya na tare da su, kuma a shirye suke ba su goyon baya a kowane lokaci.
Ya kuma bayar da shawarar cewa ya kamata gwamnoni da sarakunan gargajiya su riƙa gudanar da taruka akai-akai domin tattauna matsaloli da yanke shawara tare.
A ƙarshe, ya ce sarakunan gargajiya za su ci gaba da bayar da gudummawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Arewa da Najeriya gaba baki ɗaya.