Gobara Ta Babbake Wani Shago A Jihar Kwara
Published: 20th, March 2025 GMT
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara.
A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an samu tashin gobarar ta kira motar kashe gobara da ma’aikatanta sun isa wurin da gaggawa domin shawo kan gobarar, wadda ta kone wani shago a gaban wani gini mai daki 13.
A cewarsa duk da tsananin gobarar, jami’an kashe gobara sun yi taka-tsan-tsan, inda suka dakile tare da kashe wutar kafin ta bazu zuwa wasu gine-ginen da ke kusa.
Sanarwar ta bayyana cewa binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa wutar lantarki ce ta haddasa gobarar.
Daraktan hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Prince Falade John, ya jajanta wa mai shagon da abin ya shafa, ya kuma yi addu’ar Allah ya mayar musu da asarar da suka yi.
Ya kuma jaddada mahimmancin bin matakan tsaro don kaucewa faruwar al’amura a nan gaba.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gobara Kwara kashe gobara
এছাড়াও পড়ুন:
Ƴansanda Sun Kama Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar October 31, 2025
Manyan Labarai NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa October 31, 2025 Labarai Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda October 31, 2025