HKI Tana Tana Son Ci Gaba Da Yaki Kuma Trump Yana Tare Da Shi
Published: 8th, July 2025 GMT
Wata majiya wacce bata son a bayyana sunanta a nan Iran ta fadawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa a ziyarar da Benyamin Natanyaho yake yi a halin yanzu a kasar Amurka ya nuna cewa yana son ci gaba da yaki da kasar Iran sannan da alamun shugaba Trump yana tare da shi.
Labarin ya kara da cewa matsayin shuwagabannin biyu a yanzun bai da bambanci da matsayinsu bayan yakin kwanaki 12.
Majiyar ta bayyaa cewa Iran a shirye take ta kare kansa, kuma tana ganin ziyarar da Natanyahu yake a Amurka duk yaudara ce, saboda tuni sun rika sun yanke shawara kan ci gaba da yaki.
Dangane da sake dawowa kan teburin tattaunawa da Amurka kuma, majiyar ta ce, Idan Trump yana ganin da sauki zamu sake komawa kan teburin tattauna da shi, yana ruda kansa ne.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Olubadan Na Ibadan Ya Rasu Yana Da Shekara 90
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu, yana da shekara 90 a duniya.
Kakakin iyalan basaraken ne ya tabbatar da mutuwarsa da safiyar yau Litinin cikin wani saƙo da ya aike wa manema labarai.
Kwanaki biyu da suka gabata ne basaraken ya gudanar da bikin cikarsa shekara 90 a duniya a wani ƙasaitaccen biki da aka gudanar a fadarsa.
A shekarar da ta gabata ne aka naɗa Sarki Olakulehin a matsayin Olubadan na Ibadan bayan rasuwar wanda ya gabace shi Sarki Alli Okunmade II.