ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Nijeriya
Published: 8th, July 2025 GMT
“Wannan yajin aiki ba wata sabuwar tattaunawa ba ce,” in ji shi.
“Abin da muke yi kawai martani ne ga halin ƙunci da mambobinmu ke ciki. Ofishin Akanta-Janar na ƙasa ne ke jinkirta biyan albashin da gangan.”
ASUU ta ce ta riga ta gana da hukumomin gwamnati don bayyana matsalolinta, amma ba a ɗauki mataki ba.
Farfesa Piwuna, ya kuma ƙara da cewa har yanzu malaman jami’a na bin gwamnati Naira biliyan 10 daga cikin Naira biliyan 50 da za a biya su a matsayin haƙƙoƙinsu (Earned Academic Allowances – EAA).
Ya gargaɗi gwamnati cewa duk wata jami’a da ba a biya malamanta albashi ba, za ta ci gaba da yajin aiki har sai an warware matsalar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Gwamnatin Tarayya Yajin Aiki
এছাড়াও পড়ুন:
DSS ta cafke tsoffin jami’anta 2 kan aikata zamba
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), ta kama wasu tsoffin jami’anta biyu da ta kora daga aiki bisa zargin yin amfani da sunan hukumar wajen aikata zamba.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Laraba, ta bayyana sunayen mutanen da aka kama da Barry Donald da Victor Onyedikachi Godwin.
Ka da a ɗora wa Tinubu laifin rikicin da ke faruwa a PDP — Fayose Kotu ta daure kocin kwallon kafa a Kano shekara 8 saboda aikata luwadiDSS ta ce mutanen na amfani da sunanta suna yaudarar jama’a.
Sanarwar ta ƙara da cewa an kama su, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu domin girbar abin da suka aikata.
A baya, DSS ta gargaɗi jama’a cewa waɗannan mutane ba su da alaƙa da hukumar, domin an kore su daga aiki, kuma duk wani abu da suke yi ba ya da nasaba da DSS.