Hukumar Abinci Ta Duniya ( WFP) Ta Jefa Wa Mutanane Kudancin Sudan Abinci Ta Sama
Published: 8th, July 2025 GMT
Hukumar abinci ta duniya ta fara aikewa da kayan abinci zuwa kudancin Sudan, ta hanyar amfani da jiragen sama domin jefa kayan agaji ga mazauna Kudancin Sudan da sauran yankunan da suke a killace tun cikin watan Maris.
Tun watanni 4 da su ka gabata ne dai hukumar abincin ta duniya ta fara aikewa da kayan agaji a kudancin Sudan din, bayan da fada mai tsanani ya hana a iya bi ta hanyoyin kasa.
A gefe daya, shugabar kungiyar ta Abinci reshen Afirka Mary Elen macgroti ta ce, fada da ake ci gaba da yi a yankin ya haddasa karacin ab inci, tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa domin magance wannan matsala.
Da akwi mutane kusan miliyan daya a yankin tekun Nilu da suke fuskantar yunwa mai tsanani, wasu 34,000 daga cikinsu yanayinsu ya fi tsananta.
Tun da yaki ya barke a kasar Sudan a 2023, masu bukatuwa da taimako suke kara yawa, da hakan ya tilastawa miliyoyi yin hijira zuwa kasashen makwabta da kuma a cikin gida.
A kasar Habasha kadai da akwai ‘yan hijirar Sudan da sun kai 50,000, kamar yadda hukar ta ambata.
A cikin jahohin Nilul-A’ala, da Arewacin Junqali kadai, hukumar Abincin ta Duniya tana son kai wa mutane 470,000 taimakon abinci daga nan zuwa watan Ogusta.
Sai dai hukumar taka korafin karancin abinci, ta yadda ya zuwa yanzu yake da bukatuwa da dalar Amurka miliyan 274 daga nan zuwa karshen wannan shekara. Yunwa tana yin barazana ga rayuwar mutane miliyan 7.7 a kudancin Sudan, amma a halin yanzu, hukumar za ta iya ciyar da mutane miliyan 2.5 ne kadai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Imam Khaminae Ya Halarci Makokin Ashoora A Gidansa A Tehran
Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya halarci zaman makokin da aka gudanar a hussainiyar Imam Khomaini (q) da cikin gidansa a nan birnin Tehran a daren Ashoorah a jiya Asabar da yamma.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Hujjatul Islam Masaoud Ali wanda ya karanta makokin yana fadar cewa, kasar Iran zata dauki darasi daga Imam Hussain (a) na rashin mika kai da azzalumai.
Ya kuma bayyana yunkurin da Iraniyawa suke yi a halin yansu yana daga cikin gwagwarmayan duniya don fuskantar azzaluman duniya karkashin jagorancin HKI da Amurka.
Ya kuma kara da cewa musulunci ne yake gaba da gaba da kafircin duniya a cikin yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka jagoranta kan JMI. Kuma wannan yunkirin da sauran masu gwagwarmaya a duniya zasu ci gaba da gwagwarmaya tare da jagorancin Imam Sayyid Aliyul Khaminae. Wannan dai shi ne bayyanar Jagoran a karon farko bayan yakin kwanaki 12.
Malamin ya kara da cewa, iraniyawa ba zasu mika kai ba har zuwa nasara kamar yadda muka koya daga Imam Hussain (a) hakan a ranar Ashoorah.
A lokacinda Mahmoud Karimi zai karanta makokin an ga Imam Khaminae (H) yana fadawa Karimi wani abu a kunnensa , inda daga baya Karimin ya bayyana cewa ya umurce shi y ace, kasata zaki wanzu a zuciyata da raina.