Aminiya:
2025-07-08@23:25:43 GMT

An ƙayyade maki da shekarun shiga jami’a a Nijeriya

Published: 8th, July 2025 GMT

Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i ta Nijeriya (JAMB) ta amince da maki 150 a matsayin mafi ƙanƙantar makin da za a bai wa ɗalibai guraben karatu a jami’o’in ƙasar.

Hukumar ta ɗauki matakin ne a taronta kan tsarin bayar da guraben karatu na 2025 da ta gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.

An ceto mutum 6 daga hannun masu garkuwa a Kebbi Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC

Haka kuma, ta ce mafi ƙanƙantar maki ga kwalejojin koyon aikin jinya shi ne 140, yayin da ta ƙayyade makin samun gurbin kwalejojin ilimi da na koyon aikin noma a 100.

Alƙaluma dai sun tabbatar da cewa an samu gagarumar faɗuwa a jarawabar JAMB da aka rubuta a wannan shekara.

A yayin da JAMB ke ƙayyade mafi ƙanƙantar makin samun gurbin karatu, ita ma Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙayyade shekara 16 a matsayin mafi ƙanƙantar shekaru da ɗalibi zai kai kafin a ba shi gurbin karatu a jami’o’in ƙasar.

Ministan Ilimi, Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a wannan Talatar a yayin taron tsara fitar da guraben karatu na 2025 a ƙasar da aka gudanar a babban ɗakin taro na Bola Ahmed Tinubu da ke Abuja.

Za a shigar da ƙa’idar cika shekara 16 a cikin manhajar Hukumar JAMB da ke tantance ƙa’idojin bayar da gurbin karatu.

Haka kuma, Ministan ya ce za a yi la’akari da ɗaliban da za su cika shekara 16 ranar 31 ga watan Agustan 2025.

A bayan nan dai ana ta cece-kuce kan bai wa ƙananan yara guraben karatu a jami’o’in ƙasar, wani abu da masana ke cewa zai shafi fahimtarsu da kuma yadda za su iya jure wa wahalhalun karatun jami’a.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: mafi ƙanƙantar guraben karatu

এছাড়াও পড়ুন:

Olubabadan ya rasu yana da shekara 90

Allah Ya yi wa Sarkin Ibadan, waro Olubadan, Oba Owolabi Olakulehin, rasuwa.

Shaidu sun bayyana cewa Oba Owolabi Olakulehin ya koma ga Mahaliccinsa ne a safiyar ranar Litinin ɗin, 7 ga watan Yuli, 2025.

Ya rasu ne yana da shekaru 90 a duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki A Faɗin Nijeriya
  • NiMet Ta Yi Hasashen Cikin Watan Yulin 2025 Za A Tabka Ambaliyar Ruwan Sama A Jihohin Nijeriya 19
  • Shafin Yanar Gizo Na ADC Ya Tsaya Cak Saboda Ɗumbin Magoya Baya Masu Son Yin Rijista
  • Olubadan Na Ibadan Ya Rasu Yana Da Shekara 90
  • An Kaddamar Da Shirin Samar Da Wutar Lantarki A Jami’ar Kashere Gombe.
  • AI Zai Maye Gurbin Ayyuka Miliyan 92 A Duniya – Farfesa Pate
  • Olubabadan ya rasu yana da shekara 90
  • Ƙwallon Mata: Nijeriya Ta Lallasa Tunisiya Da Ci 3-0 A Moroko
  • Iran ta Bukaci Gudanar da Bincike Kan Sacewar jami’ar Diblomasiyyar kasar A Lebanon Shekaru 43 Da Suka gabata