Kakakin Hafsan Hafsoshin Sojin Iran Ya Ce: Iranta Dorawa Amurka Alhakin Duk Harin Da Ta Fuskanta
Published: 8th, July 2025 GMT
Kakakin hafsan hafsoshin sojojin Iran ya ce; Iran tana dora wa Amurka alhakin duk wani hari da za a kai mata
Kakakin hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Birgediya Janar Abul-fazl Shekarchi ya jaddada cewa: Iran tana dorawa Amurka alhakin duk wani harin wuce gona da iri da za a kaddamar kan kasarta.
A wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Mayadeen, Shekarchi ya bayyana cewa: Sojojin kasar Iran ba su ne suka kaddamar da harin kan wata kasa ba, amma sun mayar da martani cikin kwanaki 12 na arangama da munanan hare-hare da suka fuskanta daga mabartan ‘yan sahayoniyya makiya.
Ya kara da cewa, “An sanya wa makiya tsagaita bude wuta ne bayan da suka fuskanci munanan hare-hare daga sojojin Iran,” yana mai cewa, “Iran sakamakon karfin martanin sojojinta ne ta tilastawa makiya dakatar da yakin, ba kamar yadda suke ikirari ba, cewa su ne suka dakatar da yakin a kashin kansu, sannan kuma Iran ce karshen wacce ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka ciki kan mabarnata ‘yan sahayoniyya.”
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Tana Adawa Da Matakan Kuntatawa Na Amurka Kan Bangarorin Kasar Da Suka Shafi Harkokin Teku Da Jigila Da Ginin Jiragen Ruwa
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Kowacce Mace Tauraruwa Ce A Kasar Sin October 14, 2025
Daga Birnin Sin Shawarwarin Sin Sun Bude Sabuwar Hanyar Bunkasa Ci Gaban Mata A Duniya October 14, 2025
Daga Birnin Sin Al’ummun Kasashe Daban-Daban Sun Yabawa Shawarwarin Sin Dake Taimakawa Wajen Dunkulewa Don Hanzarta Ci Gaban Mata October 14, 2025