Aminiya:
2025-11-02@17:11:25 GMT

An ceto mutum 6 daga hannun masu garkuwa a Kebbi

Published: 8th, July 2025 GMT

Wata rundunar haɗin gwiwa ta jami’an tsaro ta samu nasarar kuɓutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su da shanu da aka sace a Jihar Kebbi.

Bayanai sun ce an sace mutanen da dabbobin ne a ƙauyukan Ukuhu da Kokanawa a Karamar Hukumar Danko Wasagu ta jihar.

‘ADC za ta mayar da APC jam’iyyar adawa a 2027’ Gwamnatin Tinubu na shirya mana zagon ƙasa — ADC

Wani daraktan tsaro a Gwamnatin Kebbi, Abdurrahama Zagga ne ya sanar wa manema labarai nasarar da aka samu a ranar Talata, inda ya ce an kai samamen ne bayan umarni da aka samu daga Gwamna Nasiru Idris bisa bayanan sirri da aka tattaro a yankin.

A cewar Zagga, tawagar jami’an tsaro ta fatattaki ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da mutanen da kuma shanun da suka sace a wani gulbi da ke iyaka da Jihar Zamfara.

“Mutane da aka ceto an mika su ga iyalansu. Kuma wannan abin farin ciki ne ga gwamna musamman a kokarin da jami’an tsaro suke yi, lamarin da zai kara inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin masarautar Zuru.”

Ya bayyana fatan da suke da shi na kawar da ɓarayin shanu da ’yan bindigar Lukurawa a yankin Zuru da Argungu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: garkuwa da mutane Jihar Kebbi

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya

Daga Ali Muhammad Rabi’u 

 

Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi  ritaya a matakin jiha da  kananan hukumomi.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.

A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.

Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da  biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.

Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • Shin Mene Ne Matsalar Liverpool A Wannan Kakar?
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Tinubu Ya Kaddamar Da Ayyuka Bakwai A Jami’ar Ilori
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • ’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Ɗaya, Sun Kama Mace Da Zargin Garkuwa Da Mutane A Dajin Kwara