Wani Fim Din Iran Mai Ya Sami Kyauta A Baje-Kolin Fina-finai Na Shanghai
Published: 8th, July 2025 GMT
Fim din Iran mai taken: Akharin Kuse Nahang” wanda Ramtin Balf ya shirya shi ya samu kyauta a baje kolin fina-finan ta Shangahi.
Shugaban ma’aikakar al’adu da koyarwar musulunci ta Iran a yankin Bu-Shehr Muhammad Hussain Zaduyan ya sanar da cewa; Fim din wanda na ilmantarwa ne, yana daga cikin fina-finai masu muhimmanci da aka fitar da shi a Iran.
Shi dai wannan bikin na baje kolin fina-finai a Shanghai an yi shi ne daga ranar 3 ga watan Yuli zuwa 7 ga gare shi a wannan shekarar ta 2025.
An yi wannan bikin ne na baje-koli ne a daidai lokacin da ake yin taron kungiyar “BRICS” da taron kasashen Asiya.
Zanduyani ya kuma ce; Fim din na Iran wanda yake Magana akan matsalar da ake fuskanta ta karewar wasu daga cikin halittun ruwa, kamar kifin “Shakes” ya sami kyautar a wurin wannan taron na baje koli wanda shi ne karo na 17.”
Karamin ofishin jakadancin Iran a kasar China wanda yake kula da yada ala’adun Iran, shi ne ya wakilci wanda ya shirya fim din wajen karbar kyautar da aka ba shi.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung
A wannan rana, a gun taron manema labarai da aka gudanar bayan kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC, Lee Jae-myung ya ce hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Sin da Koriya ta Kudu yana da matukar muhimmanci, ya kuma yi imanin cewa birnin Shenzhen na kasar Sin zai karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC cikin nasara a shekara mai zuwa.(Safiyah Ma)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA