A Karon Farko HKI Ta Yi Furuci Da Cewa Iran Ta Kai Wa Cibiyoyinta Na Soja Hare-hare
Published: 8th, July 2025 GMT
Wani jami’in sojan HKI ya yi furcu a karon farko cewa, martanin Iran ya shafi cibiyoyinta na soja.
A yau Talata ne jami’in sojan na HKI ta yi furuci irinsa na farko cewa martanin da Iran ta mayar a watan da ya shude, ya shafi sansanonin soja.
Kamfanin dillancin labarun “Reuters” ne ya ambato jami’in sojan na ‘yan sahayoniya yana yin wannan sharadin bisa sharadin kar a ambaci sunansa.
Harin wuce gona da iri na HKI a ranar 13 ga watan Yuli ya shafi kwamandojin soja da masana fasahar Nukiliya.
Martanin jamhuriyar musulunci na Iran akan kallafaffen yakin HKI ya shafi cibiyoyin soja, leken asiri, wuraren binciken masu alaka da soja.
Iran ta yi amfani da jiragen yaki marasa matuki da kuma makamai masu linzami mabanbanta wajen kai wa HKI hari.
HKI ce ta bukaci a tsagaita wutar yaki ta hanyar Amurka, wacce ita kuma ta tuntubi kasashe masu shiga Tsakani.
An yi kirdadon cewa, asarar da HKI ta yi, ta kai ta Dala biliyan 5.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kasar Iran Ta Yaba Da Kungiyar BRICS Saboda Yin Tir Da HKI A Yakin Kwanaki 12
Ministan harkokin wajen kasar Iran wanda yake halattan taron kungiyar raya tattalin arziki ta Bricks ya yabawa kungiyar kan yin tir da Amurka da kuma HKI kan keta hurumin kasar da yaki na kwanaki 12 da kuma da kuma kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar ta zaman lafiya wadanda suke Fordo Natanz ta kuma Esfahan.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ya nakalti ministan yana fadar haka a taron kungiyar karo 17 wanda ke gudana a hilin yanzu a birnin Rio De jenero na kasar Brazil.
A ranar 13 ga watan Yunin da ya gabata ne jiragen yaki na HKI suka kutsa cikin Iran inda suka kashe manya-manyan kwamandocin sojojin kasar da kuma masana fasahar Nukliyar kasar ga shahada.
Bayan haka sojojin yahudawan sun kai hare-hare kan tashar talabijin ta “Khabar” na harshen farisanci a hukumar tashoshin radio da talabijin na kasar.
Banda haka jiragen yakin Amurka B-2 sun kai hare0hare kan cibiyoyin Nukliyar kasar guda ukku.