Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a Abuja
Published: 20th, March 2025 GMT
Asibitin Ƙasa da Asibitin Asokoro da ke Abuja sun cika maƙil da mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tankar gas da ta auku da daren Laraba a gadar Karu.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:14 na dare, bayan wata babbar mota ɗauke da gas ta yi hatsari, tare da faɗawa kan wasu motoci da ke kan gadar, lamarin da ya haddasa gobara.
Rahotanni sun nuna cewa an rasa rayuka da dama, yayin da mutane da yawa suka samu munanan raunuka.
Shugaban Sashen Ɗaukar Matakan Gaggawa na Hukumar Kula da Harkokin Gaggawa ta Ƙasa (FEMA), Mista Mark Nyam, ya bayyana cewa jami’an hukumar sun isa wajen domin ceto mutanen da abin ya shafa.
Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya da ta Babban Birnin Tarayya, ’Yan Sanda, da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) sun duƙufa wajen kai ɗauki.
Wasu daga cikin waɗanda suka jikkata an kai su Asibitin Fadar Shugaban Ƙasa domin samun kulawar gaggawa.
Shirin Inganta Amfani da Gas (PCNG) na Fadar Shugaban Ƙasa, ya bayyana jimaminsa game da wannan hatsari.
Ya yi alƙawarin gudanar da bincike don gano musabbabin aukuwar lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa tankar gas ɗin ta samu matsalar birki, wanda hakan ya haddasa fashewar tankin mai.
A cikin wata sanarwa, PCNG ya buƙaci jama’a da su guji yaɗa jita-jita har sai an kammala bincike.
Hakazalika, ya jaddada aniyarsa na tabbatar da aminci wajen amfani da CNG, tare da ɗaukar matakan hana aukuwar irin wannan hatsari a nan gaba.
Jami’an agaji sun ci gaba da aikin ceto da bayar da taimako ga waɗanda lamarin ya shafa, tare da ƙoƙarin shawo kan ɓarnar da gobarar ta haifar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gobara Hatsari Karu
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Yi Ganawar Sirri da Gwamnonin Jihohi Shidda
Daga Bello Wakili
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ganawar sirri da gwamnonin jihohi shidda daga sassan ƙasar a ci gaba da tattaunawar da ake yi domin ƙarfafa batun tsaro a ƙasa.
Gwamnonin da suka halarci taron sun hada da Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo, Umar Namadi na Jigawa, Nasir Idris na Kebbi, Ahmed Ododo na Kogi, Lucky Aiyedatiwa na Ondo, da Ahmed Aliyu na jihar Sokoto.
Taron, wanda ya ɗauki kusan mintuna 40, ya mayar da hankali ne kan muhimman matsalolin tsaro da ke shafar jihohinsu, duk da cewa ba a bayyana cikakkun bayanai ba.
Wakilin Rediyon Najeriya da ke fadar shugaban kasa ya ruwaito cewa wannan zaman na daga cikin kokarin shugaban kasa na ƙara haɗin kai da jihohi wajen magance matsalolin tsaro.
Wannan cigaban ya biyo bayan nasarar da Gwamnatin Tarayya ta samu na kubutar da dalibai 100 da aka yi garkuwa da su a Jihar Neja, baya ga wanda aka yi a Jihar Kebbi.
Ci gaba da irin waɗannan tattaunawa na shugaban kasa na nuna jajircewar gwamnati wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin ƙasar.