Aminiya:
2025-11-02@16:57:48 GMT

Dukan farar hula saboda sanya kayan sojoji kuskure ne — Janar Chibuisi

Published: 28th, April 2025 GMT

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa kuskure ne abin da jami’anta ke yi na cin zarafi da cin zalin fararen hula saboda sun sanya kayan sojoji.

Shugaban Sashen Hulɗar Sojoji da Fararen Hula na rundunar, Manjo-Janar Gold Chibuisi, bayyana cewa rundunar tana hukunta duk jami’inta da aka kama da laifin cin zalin farar hula saboda sanya kayan sojoji.

Ya ce duk da haka doka ta haramta wa fararen hula sanya kayan sojoji ba bisa ka’ida ba, kuma laifi ne da zai iya kai su gidan yarin.

Manjo-Janar Gold Chibuisi, ya ci gaba da cewa doka ba ta ba ta ba sojoji ikon hukuntawa balantana cin zalin masu aikata hakan ba. Sai kuma ta ba su ikon kama masu sojan gona da kayansu, kuma an ba sojoji horo a kan kama masu aikata hakam, su miƙa shi ga ’yan sanda domin gurfanarwa a gaban ƙuliya.

Aminu Bayero ya naɗa Sanusi a matsayin Galadiman Kano NAJERIYA A YAU: “Dalilin da muke sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki”

“Duk waɗannan abubuwan — na cin zalin da cin zarafin da sojoji ke yi wa masa sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba — ba daidai ba ne. Muna kuma wayar da kansu a game da hakan, sa’annan duk sojan muka samu hujja a kansa kuma, muka yi masa hukunci mai tsanani,” in ji shi.

‘Sanya kaya soja haramcin ne ga fararen hula’

Sai dai kuma Manjo-Janar Gold Chibuisi ya yi gargadi ’yan Najeriya su guji sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba, yana mai cewa mutunta kayan sojo wani muhimmin sashi ne na ƙarfafa tsaron ƙasa.

Ya jaddada cewa yin amfani da kayan aikin soja ba bisa ƙa’ida ba ga mutanen da ba su da izini ya saɓa wa doka kuma yana taimakawa ayyukan laifi, yana mai cewa bin irin wannan shawarar zai samar da yarda tsakanin sojoji da jama’a.

Ya yi wannan gargaɗin ne a Abuja a ƙarshen mako a wani taron tattaunawa da ’yan jarida, inda ya ce, “Sanya kayan sojoji ga mutumin da ba soja ba ya saɓa wa dokar ƙasa. Idan kai ba soja ba ne ko jami’in tsaro, yin amfani da unifom ɗinsu — ko kana son sa ko ba ka so — laifi ne.”

Chibuisi ya jaddada cewa dole ne a mutunta doka don kiyaye mutunci da tsaron rundunonin soji, yana mai gargadin cewa masu aikata laifin na iya fuskantar ɗauri a kurkuku.

“Idan kuna son aikin soja, ku shiga aikin soja. Kada ku saka kayanmu idan ba a cikinmu kuke ba,” in ji shi.

Game da haɗarin tsaro da ake tattare da sanya kayan sojoji ba bisa ƙa’ida ba, Chibuisi ya bayyana cewa masu aikata laifuka na ƙara amfani da kakin soja don aikata laifuka, wanda ya sa ya zama da wahala ga fararen hula da hukumomin tsaro su gane sojojin gaske da na bogi.

Ya ce, “A halin yanzu, akwai ’yan fashi da yawa da ke amfani da kayan soji don aikata laifuka. Idan mutane suka ci gaba da yin ado da kayan sojoji, ta yaya za ku bambance tsakanin ɗan fashi da sojan gaske?”

Ya yi kira ga iyalai da al’ummomi da su taimaka wajen wayar da kan jama’a daga matakin gida.

“Idan wani da kuka sani ba ne ya fito sanye da ku ce masa, ‘Dakata, yau ka shiga aikin soja, cire wannan abin mana.’ Ka guji a kama ba.”

Janar din ya ci gaba da bayanin cewa an horar da sojoji don kama fararen hula da aka samu sanye da kayan soja kuma a miƙa su ga ’yan sanda don gurfanar da su a gaban kotu.

Ya kuma jaddada mahimmancin hana aikata laifin kafin ya faru: “Wani gefen shi ne sojojinmu su yi abin da ya dace idan sun ga haka, ɗayan gefen kuma shi ne fararen hula kada su yi hakan kwata-kwata.”

Yayin da yake bayyana bambanci tsakanin Najeriya da sauran ƙasashe a kan wanna batu, Manjo-Janar Chibuisi ya ƙara da cewa, “Nan ba Amurka ba ce. Ba za ku ce saboda fararen hula na sanya kayan sojoji a Amurka, a nan ma dole ya kasance haka. Ƙari ga haka, ƙalubalen da muke fuskanta a nan, ba na tunanin suna da su a Amurka.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: farar hula fararen hula kayan soji Kayan sojoji sanya kayan sojoji ba bisa fararen hula Manjo Janar Chibuisi ya

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar

Shugaban Lebanon Joseph Aoun ya yi Allah wadai da keta hurumin kasarsa da Isra’ila ke yi a kudancin kasar, yana mai kira da a dauki tsauraran matakai kan duk wani kutse da sojojin mamaye za su yi a nan gaba a cikin Lebanon.

A lokacin wata ganawa da Kwamandan Rundunar Soja Rodolphe Heikal, Shugaba Aoun ya bayyana cewa dole ne Lebanon ta “fuskanci duk wani kutse da Isra’ila ta yi wa yankunan kudancin da aka ‘yantar don kare filayenmu da kuma tsaron ‘yan kasa.”

Wannan jawabi ya zo ne bayan harin da Isra’ila ta kai wa gundumar Blida, inda sojojin Isra’ila suka kashe wani ma’aikacin gundumar a lokacin wani hari da suka kai kan ginin ofishin karamar hukuma.

Daga baya, karamar hukumar ta tabbatar da cewa Ibrahim Salameh, wanda ya kwana a cikin ginin, ya yi shahada bayan da sojojin mamaya suka harbe shi. Aoun ya yi Allah wadai da kisan, yana mai cewa wani bangare ne na ayyukan “Isra’ila” kan fararen hula kuma ya zo ne ‘yan sa’o’i bayan taron da kwamitin da ke sa ido kan yarjejeniyar dakatar da fadan ya gudanar.

0Please leave a feedback on thisx

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Amurka ta sanya Najeriya cikin ƙasashen da ake yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Rundunar Sojin Nijeriya Ta Shirya Wa Janar Musa Faretin Gama Aiki
  • Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar
  • Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure
  • Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu
  • Borno ta fara fitar da kayan robobi zuwa ƙasashen waje – Zulum
  • Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai