Ya isa haka: Tinubu ya umarci shugabannin tsaro su kawo ƙarshen kashe-kashe
Published: 24th, April 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba da umarnin gaggawa da a yi cikakken sauyi ga dabarun tsaron ƙasa, yana mai umartar shugabannin tsaro su ɗauki matakan gaggawa don daƙile ƙaruwar tashin hankali da kashe-kashe jihohin Borno, Filato, Binuwai, da Kwara.
Tinubu, wanda ya gana da shugabannin tsaro a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce dole ne a kawo ƙarshen kashe-kashe a jihohin da abin ya shafa.
“Ya isa haka,” in ji Shugaba Tinubu yayin da ya sake yin tir da kai hari ga ’yan Najeriya ba tare da wani dalili ba.
Mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Nuhu Ribadu, ya shaida wa manema labarai cewa shugabannin tsaron sun yi wa shugaban ƙasa cikakken bayani kan halin da tsaro ke ciki.
Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji Nijar, Mali da Burkina Faso sun kafa gidan rediyo na haɗin gwiwa NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka KasuwanciRibadu ya ce Shugaba Tinubu ya ba da umarnin amfani da sabbin dabaru don magance matsalolin rashin tsaro.
Ya ce, shugaban ƙasar “ya ba mu damar zuwa mu sake yi masa bayani. Ya ɗauki lokaci mai tsawo muna masa cikakken kan abin da ke faruwa.
“Ko da ya yi tafiya ƙasar waje yana yawan tuntuba, yana ba da umarni kuma yana bin diddigin abubuwan da ke faruwa. A yau kuma mun sami damar sake yi masa bayani na tsawon awanni.
“Mun saurara, kuma mun karɓi sabbin umarni daga gare shi. Gaskiya, ya nace cewa mu yi aiki tuƙuru don maido da tsaro a ƙasa.
“Mun yi masa bayani kan abin da ya faru kuma muka tabbatar masa da jajircewarmu.
“Mun aiwatar da umarninsa, mun je wuraren da ake fama da rashin tsaro, kamar jihohin Filato da Binuwai da Borno, kuma mun ba shi ra’ayinmu saboda ya ba mu umarni mu je mu gana da hukumomin siyasa a can,” in ji shi.
Ribadu ya ce Tinubu ya jaddada buƙatar ƙara shigar da ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi wajen magance al’amuran rashin tsaro.
“Matsalar rashin tsaro sau da yawa ba ta tsaya ga manyan matakai kawai ba. Ta ƙunshi ƙananan hukumomi. Su ne ke tare da mutane kai tsaye, musamman ma idan wasu ƙalubalen sun shafi matsalolin al’umma.
“Muna buƙatar yin aiki da al’ummomi da ƙananan hukumomi da kuma gwamnoni. Shugaban Ƙasa ya ba da umarni cewa mu ƙara yin aiki da gwamnoni,” in ji shi.
Ribadu ya ce Shugaban Ƙasa ya “damu sosai” a taron kuma ya ce “abin ya isa haka.”
Ribadu ya ce maharan galibi suna kai hari ne kan ’yan ƙasa marasa galihu ta hanyar dasa bama-bamai da kuma kai hari kan wuraren da ba su da gwamnati.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tsaro shugabannin tsaro Shugaban Ƙasa Ribadu ya ce rashin tsaro ba da umarni
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaba Tinubu Ya Taya Sabon Firaiministan Kanada Mark Carney Murna
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Mista Mark Joseph Carney murna bisa zaɓensa a matsayin Firaiminista na 24 na ƙasar Kanada, bayan nasarar jam’iyyar Liberal a zaɓen majalisar dokokin da aka kammala kwanan nan.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana zaman Carney a wannan matsayi a matsayin wani muhimmin ci gaba, musamman a wannan lokaci da Kanada ke bukatar gogaggen shugaba domin fuskantar ƙalubale da dama.
Carney, wanda fitaccen masani ne a fannin tattalin arziki, ya taba rike mukamin Gwamnan Babban Bankin Kanada daga shekarar 2008 zuwa 2013, sannan ya ci gaba da zama Gwamnan Babban Bankin Ingila daga 2013 zuwa 2020.
Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar cewa ƙwarewar sabon shugaban Kanada a fannin kuɗi da shugabanci za ta taka muhimmiyar rawa wajen gina makomar ƙasar. Haka kuma, ya sake jaddada kudirin Najeriya na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya da Kanada, musamman a fannonin ilimi, sauyin yanayi da hijira.
Shugaban Najeriya ya ƙara da cewa yana fatan kafa kyakkyawan hadin gwiwa da gwamnatin Carney, yayin da ya nuna godiyarsa ga kyakkyawar alakar da aka kula a tsakaninsu a zamanin tsohon Firayim Minista, Justin Trudeau.
Bello Wakili