Aminiya:
2025-07-23@10:53:39 GMT

An kama mutum 3 kan zargin sata da ƙone gidan bature a Gombe

Published: 27th, March 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wasu mutum uku da ake zargi da laifin sata da kuma ƙone gidan wani Bature a unguwar G.R.A, kusa da gidajen ’yan majalisa a jihar.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Hannatu Ibrahim mai shekaru 28 daga Kumo, Ahmed Adamu mai shekaru 20, da Abubakar Ibrahim mai shekaru 28.

Mutum 2 sun rasu, wani ya ji rauni a hatsarin mota a Kano Majalisa ta amince da karatu na biyu kan ƙirƙirar sabbin Jihohi 4

A cewar kakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, lamarin ya faru ne ranar 22 ga watan Maris, 2025 da misalin ƙarfe 8 na dare.

Sanarwar ta bayyana cewa Hannatu Ibrahim, wacce ke aiki a matsayin mai girki ga Mohammed Jurdi, wanda ɗan kasar Siriya da ke aiki da kamfanin Triacta Nigeria Limited, ta sace dala 35,000 (kimanin Naira miliyan 53.5) tare da banka wa gidan wuta.

Bayan samun rahoton, ‘yan sanda sun garzaya wajen, inda suka kama ta tare da gano dala 7,100 a wajenta.

A yayin bincike, ta ce Ahmed Adamu ne, mutum na farko da ta tuntuɓa bayan aikata laifin.

An samu dala 100 a cikin sakar hannunsu.

An kuma kama Abubakar Ibrahim, mai gadin gidan da aka yi satar, wanda ake zargi da taimaka musu wajen aikata laifin.

DSP Abdullahi, ya ce suna ci gaba da bincike, kuma suna shirin gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da yaƙi da laifuka tare da tabbatar da adalci a jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yar aiki zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa

Dakatacciyar Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta lashi takobin sake maka shugabancin Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio a gaban kotun daukaka kara bayan an hana ta shiga harabar majalisar a ranar Talata.

Cikin bacin rai, Natasha ta shaida wa ’yan jarida cewa za ta tattauna da lauyoyinta cikin gaggawa domin fara shigar da karar, tana mai cewa matakin ya saba da hukuncin kotun da ta bayar da umarnin a mayar da ita kan kujerarta.

Lamarin dai ya biyo bayan yadda jami’an tsaron da ke gadin majalisar suka tare hanya suka hana tawagar motocinta shiga majalisar, duk kuwa da umarnin kotu na mayar da ita.

HOTUNA: An ƙaddamar da aikin sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen $21bn a ƙetare

Ta kuma ce hatta dakatar da itan ma da farko ba ya kan ka’ida.

A cewar ta, “Yanzu zan je na tattauna da lauyoyina domin shirin daukaka kara alabasshi kotu ta fassara mana abin da ya faru. Ni mace ce mai bin dokokin kasa.”

Sanatar ta kuma yi alla-wadai da matakin da Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio ya dauka na hana ta shigar, inda ta ce hakan tamkar raina kotu ne.

Ta kuma ce, “Akpabio bai fi karfin kundin tsarin mulkin Najeriya ba. Ina so ’yan Najeriya su sani cewa ba Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa ne ya mayar da ni Sanata ba.

“Duk da cewa ya tafi daukaka kara, hakan ba yana nufin cewa ya soke hukuncin Mai Shari’a Binta Nyako ba ne kuma hakan ba zai dakatar da ni daga kasancewa Sanata ba.

“Mutanen Kogi ta Tsakiya ne suka zabe ni kuma su nake wakilta,” in ji Natasha.

Tun da farko dai Sanatar ta yi yunkurin shiga majalisar tare da magoya bayanta amma, amma aka hanata, dole sai da ta sauka ta tafi a kafa.

An dai girke tarin jami’an tsaron da ba a saba ganin irin su ba a majalisar, inda aka ga wasu jami’an na duba motoci tare da ma takaita yawan wadanda za su ajiya ababen hawa a wajen fakin na wajen majalisar.

Akalla an ga motocin sintiri na jami’an ’yan sanda guda biyar da aka girke a muhimman wuraren shiga majalisar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Pezeshkian: Tunanin Kawo Karshen Shirin Nukiliyar Iran Ya Yi Kama Da Tabuwa
  • Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa
  • UNICEF na zargin Gwamnatin Nijeriya da cin zarafin ƙananan yara
  • Yanzu-Yanzu: Majalisa Ta Amince Wa Tinubu Ciwo Bashin Dala Biliyan 21
  • Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC
  • Mutum 16 sun mutu a haɗarin jirgin sama a Bangladesh
  • Tsohon Sakataren Gwamnatin Bauchi, Ibrahim Kashim, Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
  • Kotu Ta Dage Shari’ar Zargin Cin Hanci Da Ake Yi Wa Shugaban KANSIEC Na Kano Zuwa Nuwamba
  • WHO Ta Buƙaci Isra’ila Ta Saki Ma’aikacinta Da Aka Kama A Gaza
  • Gwamnatin Kano Ta Maida Gidan Marayu Zuwa Cibiyar Gyaran Mata Masu Shaye