Sin Ta Yi Kira Da A Karfafa Hadin Gwiwa A Fannin Tattalin Arziki Na Zamani
Published: 12th, July 2025 GMT
Mataimakin firaministan Sin Ding Xuexiang, ya yi kira a karfafa hadin gwiwa a bangaren tattalin arziki na zamanni ko kuma tattalin arziki na dijital.
Ding Xuexiang ya bayyana haka ne jiya Juma’a, yayin da ya halarci bikin bude taron kungiyar kasashen hadin kai ta Shanghai (SCO) kan tattalin arzikin dijital, a birnin Tianjin dake arewacin kasar Sin.
Cikin jawabinsa na bude taron, Ding Xuexiang wanda kuma mamba ne na kwamitin dindindin na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, bisa la’akari da damarmaki da kalubale da na’urori da fasahohin zamani suka zo da su, ya kamata a yi kokarin gaggauta aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen SCO suka cimma da kuma yarjejeniyar tafiyar da harkokin fasahohin zamani ta duniya.
Mataimakin firaministan ya kuma bayar da shawarar inganta hadin gwiwa a bangaren tattalin arziki na dijital da karfafa manufofin tuntubar juna da tsara burinkan ci gaba na kasashen ta yadda za su dace da juna da yin cikakken amfani da dandamalin hadin gwiwa kamar na taron na SCO kan tattalin arzikin dijital, domin kara wa kokarin raya bangaren kuzari. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa
Ya ce manufofi da sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya aiwatar cikin shekaru biyu da suka gabata sun ƙara wa jama’a ƙwarin gwiwa game da tattalin arziƙin ƙasa da tafiyar da gwamnati, abin da ya sa zai yi wuya a kayar da shi a 2027.
“Babu wani ɗan siyasa a yau da zai iya ƙalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Muna tafiya da ‘sabon fata’ zuwa ‘farfafowa,’ kuma wannan farfaɗowar dole ne ta bayyana a rayuwar talakawa,” in ji Bwala.
Ya ƙara da cewa shugabannin ƙungiyoyi daga dukkanin shiyyoyi shida na ƙasar nan sun halarci taron, ciki har da wasu da suka zo daga Biritaniya.
Bwala, ya bayyana cewa taron ba yaƙin neman zaɓe ba ne, amma wata dama ce don gina kyakkyawar alaƙa tsakanin gwamnati da abokan hulɗa na ƙasa.
“Wasu mutane suna jiran lokacin zaɓe kafin su nemi ƙungiyoyi, amma wannan ba daidai ba ne. Ba kayan aiki ba ne, abokan tafiya ne, dole su kasance cikin abin da gwamnati ke yi,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan taruka za a shirya su a Biritaniya, Amurka da Kanada don tattaunawa da ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje da kuma yaɗa bayanai game da nasarorin gwamnatin Tinubu.
Bwala, ya bayyana cewa Fadar Shugaban Ƙasa tana shirin gudanar da babban taron tattaunawa a watan Nuwamba, inda dukkanin ƙungiyoyi za su haɗu domin nazarin dabarunsu da kuma kimanta yadda gwamnati ke aiki.
Ya ce sauye-sauyen tattalin arziƙi da gwamnatin Tinubu ta fara aiwatarwa sun fara bayar da sakamako a fannoni daban-daban kamar makamashi, noma, ayyukan gina ƙasa da samar da ayyukan yi.
“Mun riga mun fara ganin sakamako. Idan muka je fagen aiki, za mu ga ci gaba a bangaren tattalin arziƙi, tsaro, ilimi da noma. Waɗannan ƙungiyoyi za su ci gaba da yaɗa wannan saƙo,” in ji shi.
Shi ma tsohon ɗan majalisa, Hon. Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, wanda ya halarci taron, ya yaba wa jagorancin Tinubu.
“Ko mutum ya so ko ya ƙi, Shugaban Ƙasa zai sake lashe zaɓe a 2027. Ba mu kai inda muke so ba tukuna, amma muna cimma nasara. Shugaban Ƙasa na yin duk abin da zai yi don kawo ci gaba,” in ji shi.
Agbonayinma, ya kuma yaba da cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya ba da damar a saki maƙudan kuɗaɗe don jihohi su inganta ci gaban al’umma a matakin ƙasa.
Dukkanin masu jawabin sun buƙaci ƙungiyoyin su ci gaba da yaɗa manufofin gwamnati da kuma tabbatar da haɗin kai tsakanin yankuna da jam’iyyu.
Bwala, ya kuma buƙaci magoya bayan Tinubu su ci gaba da nuna goyon baya da ƙauna ga Shugaban Ƙasa.
“Shugaba Tinubu ya yi abin da ya cancanci ba kawai goyon bayan jama’a ba, har ma da soyayya da jajircewarsu don ci gaba da abin da gwamnatinsa ta fara,” in ji shi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA