Kasar Sin Na Fatan EU Za Ta Yi Aiki Da Ita Bisa Alkibla Guda Da Tsara Hadin Gwiwa Na Shekaru 50 Masu Zuwa
Published: 22nd, July 2025 GMT
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana a yayin gudanar da taron manema labaru na yau da kullum da aka yi yau Litinin cewa, bana shekara ce ta cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Tarayyar Turai EU. Kuma taron kolin kasar Sin da EU karo na 25 na karatowa.
Bayan cimma yarjejeniya tsakanin Sin da kungiyar EU, shugaban majalisar Tarayyar Turai António Costa da shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, za su ziyarci kasar Sin a ranar 24 ga watan Yuli. Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai gana da shugabannin na EU guda biyu. Kazalika, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai jagoranci taron koli na Sin da EU karo na 25 tare da shugabannin kungiyar ta EU guda biyu.
Bugu da kari, wasu jami’an diflomasiyyar Turai sun bayyana cewa, kasar Sin na kokarin yin amfani da damar sake fasalin hukumomi don bikin cika shekaru 80 da kafuwar MDD wajen fadada tasirinta a MDD. A yayin da yake mayar da martani kan wannan batu, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin na son yin hadin gwiwa tare da kasashen Turai wajen daukar bikin cika shekaru 80 da kafuwar MDD a matsayin wata dama ta kara karfafa muhimmin matsayin da MDD take da shi, da taka rawar da ta dace a matsayinta na MDD yadda ya kamata, da sanya kwarin gwiwa da karfafa damawa da bangarori daban daban. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Xi: A Hada Kai Wajen Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Ban da haka, shugaban na Sin ya ce, kasarsa na son yin kokari tare da bangarori daban daban, wajen aiwatar da ra’ayin raya kasa na kirkiro sabbin fasahohi, da tabbatar da daidaito, da kare muhalli, da bude kofa, gami da haifar da alfanu ga kowa, ta yadda za a kafa wata al’ummar bai daya ta yankin Asiya da na tekun Pasifik.
Duk a wajen taron, yayin wani bikin mika damar karbar bakuncin taron kungiyar APEC, shugaba Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta karbi bakuncin kwarya-kwaryar taron shugabannin kungiyar APEC karo na 33, wanda ake sa ran gudanar da shi a birnin Shenzhen na kasar Sin a watan Nuwamba na shekarar 2026. (Bello Wang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA