Albarkacin taron ministocin kasa da kasa na tattauna mu’ammalar wayewar kai ta duniya, CGTN ta hada hannu da jami’ar Renmin ta kasar Sin, domin jin ra’ayin al’ummun kasashe 41 da yawansu ya kai dubu 12.

Masu bayyana ra’ayoyin na ganin cewa, mu’ammala, da cudanyar al’adu, da wayewar kai muhimmin karfi ne na ciyar da bunkasar wayewar kan daukacin bil’adama da zaman lafiyar duniya gaba, don haka ne ma darajanta al’adu da magabata suke dora muhimmanci a kanmu, da kirkire-kirkire, na da babbar ma’ana ga zamanantar da al’ummun bil’adama, wanda hakan ya sa shawarar bunkasa al’adun duniya da Xi Jinping ya gabatar, ta samu karbuwa tsakanin sassan kasashe daban-daban, yayin da suke kokarin tinkarar kalubaloli a duniya.

Yayin da aka tabo batun fahimtar alamun al’adun Sinawa, kashi 60.6% daga cikin mutanen da aka jin ra’ayinsu, na mai da batun kirkire-kirkire a gaban komai. A ganinsu kirkire-kirkire a bangaren kimiya na jawo hankulansu matuka. Kazalika, kaso 77.2% daga cikinsu sun fi mayar da matukar hankali kan kimiyar Sin, da yadda ake amfani da ita, fiye da mayar da hankula kan zamantakewar Sinawa, da al’adun gargajiya, da al’adu na zamani na kasar Sin. Dadin dadawa, kaso 81.6% daga cikinsu na ganin cewa, tasirin al’adun Sin sun rika karuwa a duniya, kuma fiye da kashi 80% na matasan da aka ji ra’ayinsu ’yan kasa da shekaru 44, su ma sun amince da wannan ra’ayi. Kana kashi 70.6% na ganin cewa, wayewar kan Sinawa, ta bullo da wata sabuwar hanyar daidaita harkokin duniya. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Abinci Ta Duniya ( WFP) Ta Jefa Wa Mutanane Kudancin Sudan Abinci Ta Sama

Hukumar abinci ta duniya ta fara aikewa da kayan abinci zuwa kudancin Sudan, ta hanyar amfani da jiragen sama domin jefa kayan agaji ga mazauna Kudancin Sudan da sauran yankunan da suke a killace tun cikin watan Maris.

Tun watanni 4 da su ka gabata ne dai hukumar abincin ta duniya ta fara aikewa da kayan agaji a kudancin Sudan din, bayan da fada mai tsanani ya hana a iya bi ta hanyoyin kasa.

A gefe daya, shugabar kungiyar ta Abinci reshen Afirka Mary Elen macgroti ta ce, fada da ake ci gaba da yi a yankin ya haddasa karacin ab inci, tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa domin magance wannan matsala.

Da akwi mutane kusan miliyan daya a yankin tekun Nilu  da suke fuskantar yunwa mai tsanani, wasu 34,000 daga cikinsu yanayinsu ya fi tsananta.

Tun da yaki ya barke a kasar Sudan a 2023, masu bukatuwa da taimako suke kara yawa, da hakan ya tilastawa miliyoyi yin hijira zuwa kasashen makwabta da kuma a cikin gida.

A kasar Habasha kadai da akwai ‘yan hijirar Sudan da sun kai 50,000, kamar yadda hukar ta ambata.

A cikin jahohin Nilul-A’ala, da Arewacin Junqali kadai, hukumar Abincin ta Duniya tana son kai wa mutane 470,000 taimakon abinci daga nan zuwa watan Ogusta.

Sai dai hukumar taka korafin karancin abinci, ta yadda ya zuwa yanzu yake da bukatuwa da dalar Amurka miliyan 274 daga nan zuwa karshen wannan shekara. Yunwa tana yin barazana ga rayuwar mutane miliyan 7.7 a kudancin Sudan, amma a halin yanzu, hukumar za ta iya ciyar da mutane miliyan 2.5 ne kadai.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Jinping Ya Aike Da Sakon Taya Murnar Bude Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adam
  • An Bude Taron Ministoci Kan Wayewar Kai A Birnin Beijing
  • An Fara Taron Nishan Karo Na 11 Game Da Wayewar Kai A Duniya
  • Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense
  • Firaminsitan Sin: Dole Ne Hadin Gwiwar Brics Ya Gaggauta Kafa Ka’idar Ciniki Da Tattalin Arzikin Duniya Mai Adalci Da Bude Kofa
  • Babatun Lai Ching-Te Ba Zai Taba Girgiza Kasancewar Sin Day Tak A Duniya Ba
  • Hukumar Abinci Ta Duniya ( WFP) Ta Jefa Wa Mutanane Kudancin Sudan Abinci Ta Sama
  • Sin Za Ta Yi Aiki Da MDD Don Samar Da Jagorancin Duniya Mai Cike Da Adalci Da Daidaito
  • Zan Yi Ƙoƙarin Dawo Da Martabar Kano Pillars A Idon Duniya — Ahmed Musa