Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma
Published: 12th, July 2025 GMT
Har ila yau, manufar ita ce; don rage yawan asarar da manoma ke tabkawa, bayan sun yi girbin farko da kuma jawo hankalin matasan kasar, domin su rungumi aikin na noma; musamman wanda za su yi, su samu riba.
Kaddamar da Taraktocin na zuwa ne, daidai da lokacin da kasar ke ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci, wanda ya kai sama da kashi 30 cikin 100, duba da cewa; noman da ake yi a karkara na ci gaba yin karanci.
Idan har an rabar da wadannan Taraktoci yadda ya dace tare da horar da manoman da za su amfana, an kuma tabbatar da ana bai wa Taraktocin kulawar da ta kamata da sayar da su cikin rahusa, hakan zai taimaka wajen samun kyakkyawan sauyi a fannin noman kasar, musamman a bangaren samun riba.
Sai dai, har yanzu; tambayar da ake ci gaba da yi ita ce, shin ko wannan shiri zai samar da kyakkyawan sauyi a fannin na aikin noman kasar?
Hakikanin Fannin Aikin Noma Don Samun Riba A Nijeriya:
Fannin aikin noman kasar, na samar da ayyukan yi sama da kashi 70 cikin 100, inda kuma fannin ya kasance kimanin kashi 34 cikin 100 na aikin da ake yi a kasar.
Amma duk da haka, har yanzu fannin kashi 26 kacal yake bayarwa a matsayin gudunmawa, don bunkasa tattalin arzikin kasar, wanda akasari hakan na faruwa ne, sakamakon yadda ake yin noma da kayan aiki na gargajiya.
Nijeriya da ke Afirka ta Kudu da Hamada, aikin nomanta ya yi kasa sakamakon rashin yin aiki da kayan noma na zamani. Ta kuma kasance, tana da kasa da karamin ma’auni na hekta da ya kimanin 0.3, wanda hakan ya saba da shawarar da Hukumar Kula da Abinci da Ayyukan Noma ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO) ta bayar na bukatar samar da hekta 1.5 na yin noma.
Bugu da kari, an rawaito Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa; Nijeriya mai yawan al’umma sama da miliyan 210, amma abin takaici, kasar na da Taraktocin noma masu aiki daga tsakanin 7,000 zuwa 12,000 ne kacal.
A cewarsa, hakan ya sanya a shekaru da dama da suka gabata, aka gaza samun bukatar da ake da ita ta samar da yawan abincin da ya kai mililiyan 2.4, domin bukatar ‘yan kasar.
Sai dai, ana ganin bisa wannan sabon yunkuri na gwamnatin ta hanyar hadaka da kamfanin kera kayan aikin noma da ke Belarus, wanda aka kaddamar da aikin tare da AfTrade DMCC, hakan ya sa an samar da ingantattun Taraktocin noma 2,000 tare da samar da kayan haro 190 da sauran makamantansu.
A karkashin aikin, ana sa ran za a noma hektar noma sama da 550,000, wadanda za su samar da tan miliyan 2 na hatsi tare da samar da ayyukan yi, wadanda ba na kai tsaye ba kimanin 16,000 da kuma na kai tsaye kimanin sama da 550,000.
Kaddamar da Taraktocin da sauran kayan aiki, hakan zai taimaka wajen habaka aikin noma don samun riba da kara bunkasa samar da wadataccen abinci da rage shigo da kayan abinci cikin Nijeriya, wanda yanzu haka, wadanda ake shigo da su a duk shekara, kudinsu ya kai sama da dala biliyan 2.5
Samar Da Wadataccen Abinci Da Matsalar Samun Hauhawar Farashin Kayan Abinci A Nijeriya:
Duk da samar da albarkar hektocin noma da Nijeriya ke da su, wadanda suka kai miliyan 70.8 kuma ake noma amfanin gona kamar irin su; Masara, Rogo, Shinkafa da saurasu, amma kasar na ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci.
Fannin shi ne kusan kashin bayan bunkasa tattalin arzikin kasar, amma sama da ‘yan kasar miliyan 100 ne a yanzu ke fuskantar karancin abinci, kuma suna ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan na abinci da kuma rashin wadatattun kudaden sayen kayan abincin.
Wannan adadin, ya nuna yadda yanayin hauhawar farashin ya yi kamari, musamman a Arewa ta Tsakiyar kasar, wanda ya kai kashi 29.43 a Arewa ta Gabas, ya kai kashi 29.72.
Bugu da kari, kididdiga ta nuna cewa; ‘yan Nijeriya miliyan 18.6 ke ci gaba da jure wa yunwa, inda kuma mutane miliyan 43.7, suka dauki matakin rage cin abincin da suke ciyar da iyalansu.
‘Yan Nijeriya miliyan 133 ke ci gaba da fuskantar karancin ababen more rayuwa tare da ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci, wanda a watan Mayun 2025 ya kai kashi 21.14 tare da kuma fuskantar matsananciyar yunwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan hauhawar farashin kayan abinci
এছাড়াও পড়ুন:
Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa
‘Yan sa’o’i kafin sanarwar da Jam’iyyar ta RN ta yi ne dai, tsohon Firaministansa Edouard Philippe ya ce yana goyon bayan shirya sabon zaben shugaban kasa a gaggauce.
Wannan matsin lamba dai kari ne kan wadda shugaban na Faransa ke fusakanta daga bangaren masu sassaucin ra’ayi, wadanda su kuma bukatarsu ita ce a zabi sabon Firaminista daga cikinsu.
Sai dai a iya cewa akwai ragowar fatan kawo karshen rudanin da siyasar Faransar ta shiga, la’akari da bayanan da suka ce a dazu an shiga tattaunawa tsakanin jagoran jam’iyyar masu ra’ayin ‘yan mazan jiya Bruno Retailleau da Firaminista Lecournu, kwana guda bayan murabus din da ya yi. Yayin da kuma a gefe guda rahotanni suka ce a gobe Laraba wakilan masu sassaucin ra’ayi na jam’iyyar Socialist za su gana da Firaminista Lecournun mai murabus.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA