Majiyar Diplomasiyya: Rasha Ba Ta Gabatarwa Da Iran Batun Dakatar Da Tace Sanadarin Uraniumu Ba
Published: 13th, July 2025 GMT
Kamfanin dillancin labarun “Mehr” na Iran ya nakalto cewa; Iran ba za ta amince da duk wata shawara akan ta dakatar da tace sanadarin Uranium ba wanda halartaccen hakkinta ne.”
A jiya Asabar ne majiyar diplimasiyyar jamhuriyar musulunci ta Iran ta sanar da tashar talabijin din ‘almayadin’ cewa; Tace sanadarin Uranium a cikin kasarta hakkinta ne halartacce, kuma babu sauyi a cikin matsayar Rasha dangane da haka.
Wata majiyar Rasha ta ce, gabanin harin HKI akan Iran, a lokacin da ake tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka, Moscow ta amince da a fitar da tataccen Uranium sama da daraja 3.67% daga cikin kasar Iran zuwa Rasha a matsayin bayar da tata gudunmawar na warware sabani.
A ranar 20 ga watan Yuli ne shugaban kasar Rasha, Vladmir Putin ya bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan Iran a fafutukar da take yin a kare halartattun manufofinta, a su ka hada da mallakar makamashin Nukiliya na zaman lafiya.
A ranar 11 ga watan Yuni kuwa, mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Segey Riyabkov, ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta karbi Uranium mai yawa domin taimakawa a cimma yarjejeniya a tsakanin Iran da Amurka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba
Ya kuma ce matakan takaita fitar da ma’adanan farin karfe da Sin ta dauka a baya bayan nan, ba su da alaka da kasar Pakistan. Yana cewa matakai ne da gwamnatin Sin ta dauka bisa doka da oda da nufin inganta tsarinta na fitar da kayayyaki. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA