HausaTv:
2025-10-15@05:37:19 GMT

 Dakarun Kassam Da Sarayal Kuds, Sun Kai Wa ‘Yan Mamaya Hare-hare A Gaza

Published: 13th, July 2025 GMT

Dakarun rundunar “Shahid Izzuddin al-kassam’ da kuma ” Sarayal Kuds” sun sanar da kai jerin hare-hare akan sansanonin ‘yan sahayoniya a yankuna mabanbanta na Gaza.

A bayanin da dakarun ” Kassam” su ka fitar sun bayyana hare-hare masu yawa da su ka kai wa ‘yan mamaya, da su ka hada da tarwatsa motocin buldoza biyu samfurin D9 a unguwar Zaituna a cikin birnin Gaza.

Haka nan kuma sun kai wani harin a ranar 6 ga watan Yuli wanda su ka rusa tankar yaki ta “Mirkava” ta hanyar amfani da wata nakiya mai tsananin fashewa.

Bugu da kari , Kassam ta ce a ranar 9 ga watan Yuli din ta kai wani harin akan sansanin da kwamandoji masu bayar da umarnin yaki suke a gabashin unguwar ‘al-tuffah’ a gabashin birnin Gaza,wanda ya yi wa abokan gaba asara mai yawa.

 Haka nan kuma maharban na Kassam sun yi nasarar harbe wani sojan HKI a yankin Abasan al-kabirah, a gabashin birnin Khan-Yunus dake kudancin Gaza.

 Su ma dakarun ” Sarayal-Kuds” na kungiyar Jiahdul-Islami sun sanar da jerin hare-hare akan sansanoni mabanbanta na ‘yan sahayoniya da su ka hada da rusa motocin yaki irin su tankar “Mirkava’ a unguwar ‘ al-Tuffah’ a cikin birnin Gaza. Haka nan kuma dakarun sun sanar da rusa wata motar ta soja a cikin Gaza.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa

Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar.

Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta.

Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako.

Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista da kungiyar domin kasacewa a karkashin inuwa daya ta yadda za su ci moriyar tanade tanaden ta, sannan su kasance masu mutunta shugabanci da kuma bin doka da oda domin inganta rayuwar su.

Ya ce yayin da kungiyar ta ke da ‘yan dako kimanin dubu 20 a karkashin ta, akwai bukatar duk ‘yan dakon da ba su da katin zabe su karbi sabo ko kuma su sabunta wanda ya bata ko ya lalace domin amfani da damar su wajen zaben shugabanni.

A sakon sa, Hakimin Maigatari Alhaji Sani Alhassan Muhammad wanda ya sami wakilcin Sarkin Kasuwar Maigatari Alhaji Muhammadu Sarkin Kasuwa, ya bukaci sabon sakataren kungiyar Malam Muhammad Tajudeen ya kasance mai nuna gaskiya da adalci wajen huldar sa da ‘yan dako da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci, inda ya bayyana murnar samun wannan mukamin.

Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Sarkin hatsin Maigatari, Malam Mu’azu Bako da Shugaban leburorin Dingas na Jamhuriyar Nijar Malam Lawwali Hassan.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ya kamata ‘yan fim su rika taimaka wa kananan cikinsu-Rukayya Abdullahi
  • Iran Ta Jadda Cewa A Shirye Take Ta Kare Kanta A Duk Wani Yaki Wanda Makiya Zasu Dora Mata
  • Ana Gudanar Da Taron Masu Mukamin Magajin Gari Na Kasa Da Kasa A Birnin Dunhuang Na Sin
  • Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba
  • Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa
  • Ahmed Musa Ya Nemi Afuwar Ƙungiyar 3SC Akan Abinda Ya Faru Da ‘Yan Wasansu A Kano
  • Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
  • Ƴan Bindiga Sun Amince Da Dakatar Da Hare-Hare A Ƙananan Hukumomi 5 A Katsina
  • Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon
  • Macron Na Ci Gaba Da Shan Matsin Lamba Daga ‘Yan Adawa Da Tsofaffin Na Hannun Damansa