2025-07-12@14:49:21 GMT
إجمالي نتائج البحث: 26
«ɗan kasuwar»:
Gwamnatin Jihar Neja, ta rufe Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBBU) da ke Lapai saboda matsalolin tsaro da suka janyo mutuwar wasu ɗalibai. Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Usman, ya ce an ɗauki wannan matakin ne saboda rashin tabbacin tsaro da ke barazana ga rayuwar ɗalibai da ma’aikata. Yadda na kuɓuta daga harin Filato — Wani mutum 1447: Yau ce ranar sabuwar shekarar Musulunci – Sarkin Musulmi Gwamna Umaru Bago ya amince da rufe jami’ar nan take, kuma za ta ci gaba da kasancewa a rufe har sai an samu sauyi. “Lafiyar kowa, musamman ɗalibai da malamai, na da matuƙar muhimmanci ga gwamnatin Jihar Neja,” in ji sanarwar. “Mun yi matuƙar baƙin ciki da abin da ya faru, kuma muna ɗaukar matakan...
’Yan Najeriya mazauna ƙasar Isra’ila sun maƙale bayan ɓarkewar yaƙin Iran da Isra’ila. Sun nemi agajin Gwamnatin Tarayya game da kan halin ƙuncin da suka faɗa tun bayan ɓarkewar yaƙi. Cikin wani rahoto da Jaridar Punch ta wallafa, ’yan Najeriyar sun zargi gwamnati da rashin kai masu ɗauki yadda da ya kamata, inda suka ce tuni sauran ƙasashe suka fara kwashe ’yan ƙasarsu. Rahoton ya bayyana cewa ’yan Najeriyar sun fi yawa a birnin Ƙudus da Tel Aviv, inda Iran ta tsananta kai hare-hare. A halin yanzu, mazauna Isra’ilar sun bayyana cewa suna ɓoye ne a wurare da babu tabbas kuma rayuwarsu na cikin haɗari, a koyaushe komai na iya faruwa da su.
An samu rahoton cewa guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya (Federal Polytechnic), Idah a Jihar Kogi, inda ta ɓarnata kadarori da gine-gine da dama. Rahoton na cewa, wata mummunar guguwar ruwan sama da ta biyo bayan ruwan sama da aka kwashe tsawon sa’o’i ana yi a ranar Laraba ce ta haddasa barnar, inda ta lalata rufin gine-gine da tagar gine-gine da dama a makarantar. Tinubu na ƙaddamar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna Za a dawo da dukkan Alhazai gida ranar 28 ga Yuni – NAHCON Ana cikin haka, an ba da rahoton cewa ɗakunan karatu da ɗakunan gwaje-gwaje da ɗakunan kwanan ɗalibai da ke cikin harabar kwalejin guguwar ruwan saman ta haddasa...
Shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana cewar an samu kura-kurai a sakamakon jarrabawar UTME ta shekarar 2025 da aka saki kwanan nan. A yayin wani taron manema labarai a Abuja, Farfesa Oloyede, ya fashe da kuka yayin da yake bai wa ɗalibai haƙuri, inda ya nuna nadamarsa kan wahalar da suka sha. Mutum 2 sun shiga hannu zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Gombe ’Yan bindiga sun kashe jarirai, sun bai wa karnuka namansu a Zamfara A cewar JAMB, matsalolin fasaha sun shafi sakamakon ɗalibai 379,997. Waɗannan matsaloli sun fi shafar jihohin Kudu maso Gabas da kuma Jihar Legas. A Legas, ɗalibai 206,610 daga cibiyoyi 65 ne suka fuskanci matsalar, yayin da...
Ministan Ilimi a Nijeriya, Tunji Alausa ya ce hana satar amsa ne ya janyo faɗuwar ɗalibai a jarawabar shiga manyan makarantu da JAMB ke shiryawa a kowace shekara. Tunji ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Channels a ranar Talata. ‘Raini ne ya sa ake ƙalubalantar yunƙurin kafa ƙungiyar Hausawa zalla’ Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin lura da gwamnan riƙo na Jihar Ribas Ya ce sakamakon bana da aka samu, ya nuna irin yadda aka ƙara inganta yanayin rubuta jarabawar yadda ya kamata. Ya bayyana cewa hakan kuma ya nuna yadda tsarin rubuta jarabawar ya daƙile satar amsa da ɗalibai ke yi. Alausa ya ƙara da cewa kada a ɗauki sakamakon na JAMB a matsayin koma-baya, maimakon...
Masana harkokin tsaro sun ja hankalin hukumomi su ɗauki matakan da suka dace bayan gobarar ma’ajiyar makamai a babban Barikin Sojoji na Giwa da ke Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Sun bayyana damuwa game da mummunan abin da ke iya biyo baya ta fuskoki daban-daban, tare da bayar da shawarar matakan da ya kamata a ɗauka domin daƙile ayyukan miyagu da ke iya ƙoƙarin cin gajiyar yanayin a matsayin wata dama ta aikata mugun laifi ko ta’addanci. Damuwar ƙwararru kan ƙarsashi da karfin sojoji Wani ƙwararre kan harkokin tsaro, Kabiru Adamu, ya ce illar wannan lamari ta wuce ɓarnar zahiri da kuma yiwuwar asarar rayuka. Ya ce, “Lalacewar makamai, harsasai, da sauran muhimman kayan aikin soja a barikin babban asarar...
An dawo da wutar lantarki a safiyar Talatar nan a Sifaniya da Portugal bayan katsewar da aka samu ta sa’o’i wadda ita ce mafi muni da aka gani a Turai. A jiya Litinin ce dai miliyoyin mutane suka auka cikin duhu bayan ɗaukewar wutar lantarkin a ƙasashen biyu wadda ke ci gaba da ɗiga ayar tambaya kan abin da ya haifar da ita. Za a rataye wani soja saboda laifin kashe budurwarsa Boko Haram ta kashe masu zaman makoki 7 a Chibok Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa ɗaukewar wutar lantarkin ta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama da na ƙasa da katse hanyoyin sadarwa ta wayar hannu da kuma rufe na’urorin cire kuɗi na ATM a duk faɗin ƙasashen biyu....
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
Wata ’yar kasar Jamus mai suna Alexandra Hildebrandt mai shekara 66 ta ja hankalin jama’a bayan ta haifi ɗanta na 10 ba tare da maganin haihuwa ba. Haihuwar ta faru ne a ranar 19 ga Maris a Asibitin Charité da ke Berlin da taimakon likita. Bello Turji ya kashe manoma 11 a Sakkwato ’Yan bindiga sun kashe mutane 40 a sabon hari a Filato Ta bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ta yi da Jaridar TODAY.com a ranar Laraba, 26 ga watan Maris. A cewar Hildebrandt, ta rawa wa jaririn suna Philipp, wanda ya zo da nauyin kilo 7, kuma yana cikin koshin lafiya. Ta bayyana shi a matsayin wanda ya dace da ’ya’yanta da ke da yawa, wanda...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A Najeriya ana tafka muhawara a kan yadda farashin ɗanyen man fetur yake ƙara faduwa a kasuwannin duniya. Wannan lamari dai ya haddasa damuwa a zukatan wasu ’yan ƙasar, kama daga masana tattalin arziki zuwa jami’an gwamnati, kasancewar ɗanyen mai ne mafi muhimmanci a cikin hanyoyin samun kuɗaɗen shigar ƙasar. Sai dai tambayar da wasu ’yan kasar suke yi ita ce: shin yaya wannan faɗuwar ta farashin ɗanyen mai za ta shafi rayuwar talaka? NAJERIYA A YAU: Tasirin ’Yan Uwantaka Ga Rayuwar Al’umma DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Shirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan yadda faɗuwar farashin ɗanyen man fetur zai...
Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta kaddamar da wani tsari na yanar gizo wanda zai baiwa dalibai damar shiga da duba sakamakon kammala karatunsu ta hanyar lambobi. Wannan sabon yunkuri shine karo na farko da cibiyar ta samar da sakamako ta hanyar irin wannan dandali. An sanar da shirin ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mataimakin magatakarda kuma shugaban hukumar kula da harkokin jama’a Lamara Garba Azare. A cewar sanarwar jami’ar, tsarin da myBUK Team ya kirkira kuma yana bawa ɗalibai damar dawo da sakamako kai tsaye ta hanyar amfani da sashen rajistar dalibai. Takardun sakamakon za su nuna a sarari na kowane kwasa amma dole ne ɗaliban da suka kammala shekarar ƙarshe...
Wata matashiya mai suna Aleysha Ortiz ’yar shekara 19 da ke Jihar Connecticut a Amurka ta dauki matakin shari’a a kan tsohuwar makarantar sakandaren gwamnatin da ta yi saboda gazawarta ta hanyar ba ta damar kammala karatu “da sakamako mai daraja” duk da ta kasance maras ƙoƙari. A watan Yunin shekarar bara ce, Aleysha Ortiz ta kammala karatu a Makarantar Hartford Public High School da ke Hartford, a Jihar Connecticut, inda aka karama ta, har ma ta samu gurbin karatu a kwaleji, amma yanzu ta kai karar tsohuwar makarantarta saboda sakacinta. Gidauniyar Dangote ta ƙaddamar da rabon abincin N16bn ga talakawan Nijeriya EFCC ta kama Murja Kunya kan wulaƙanta takardun Naira Matashiyar mai shekara 19 tana zargin makarantar da ta...
A lokacin da Abba Musa angon da za a daura wa aure, da wasu mutum huɗu suka kama hanya zuwa kauyen Murno daga garin Boto a Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, babu wanda ya yi tunanin cewa shi angon da ’yar uwar amaryarsa, Raihanatu Sulaiman za su rasa ransu mintoci kadan kafin a daurin auren. Kafin ɗaurin auren ne Abba Musa da Maryam Sulaiman amarya da kuma Rainahatu Sulaiman (’yar uwar amarya) da Misbahu Ahmad (abokin ango) da direban motar sun tafi garin Murno da ke da nisan kilomita 5 daga Boto domin gaisawa da ’yan uwan amaryar kamar yadda aka saba a al’adar Hausawa. Soja ya shafe mako guda da harsashi a cikin ƙwaƙwalwarsa Nijar ta kori...
An haife shi a ranar 21 ga Fabrairu, 1949, kuma ya yi karatu a Jami’ar Ohio da ke Athens a Amurka, a 1981, da Jami’ar Leicester ta ƙasar Birtaniya a 1987. Ya yi aiki a kamfanin jaridun New Nigerian, da hukumar talbijin ta NTA, da Ofishin Yaɗa Labarai na Amurka (USIS). Haka kuma ya yi koyarwa a Kaduna Polytechnic, ya yi aiki a Bankin Arewa da kuma Bankin Union inda a nan ya yi ritaya a ranar 26 ga Yuni, 2005. A cikin saƙon ta’aziyyar sa a ranar Asabar, Minista Idris ya bayyana rasuwar Malam Kabir Ɗangogo a matsayin babban rashi ga Nijeriya da fannin sadarwa a nahiyar Afirka. Ya ce: “Mutuwa ta ƙwace mana ƙwararren ma’aikaci...
Assalamu alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Da fatan Allah Ya amfanar damu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan alherai goma ga ma’aurata cikin Ramadan. 4. Salon buɗa baki Ma’aurata za su yi amfani da lokacin buɗa baki don ƙara kusanci, farfaɗo da shau’uka cikin zuciya da ɗumama sha’awa. Ma’aurata su tsara buɗa bakinsu ta yadda za su zama kamar dai su sabbin masoya ne da suka sami kansu tsundum cikin sabuwar soyayyar juna. Ramadan: Abubuwa goma ga ma’aurata Abubuwa 11 da ba a sakaci da su a Ramadan — Sheikh Daurawa Suna buɗa bakin cikin wasa da raha da tsokanar juna, ciyar da juna a baki, kallon marmasa soyayya da...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya buɗa-baki a Fadar Gwamnati da ke Abuja, inda ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar nan na kan hanya gyaruwa nan ba da jimawa ba. A yayin jawabinta, ta jaddada muhimmancin tausayi da jin-ƙai a tsakanin rayuwar ɗan adam. Wani mutum ya yanke jiki ana salla a Masallaci, ya rasu a asibiti Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha Ta buƙaci kowa ya kasance mai aikata alheri tsakaninsa da Allah, ba don neman yabo ko amincewar mutane ba. A yayin buɗa-bakin, Farfesa Azeezat Adebayo, Shugabar Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Ilorin, ta bayyana cewa tausayi da jin-ƙai su ne ginshiƙai na kyakkyawar rayuwa a tsakanin al’umma. Ta tunatar da mahalarta...
Gwamnatin Sakkwato ta buƙaci a yi adalci a binciken da ake yi kan silar rasuwar ɗan ƙwallon ƙafan nan ɗan asalin jihar, Abubakar Lawal, wanda ya rasu a satin da ya gabata kasar Uganda inda yake taka leda. Kwamishinan Matasa da Wasanni na jihar, Injiniya Almustafa Muhammad Kofar Marke ne ya sanar da hakan a lokacin da suke karbar gawar margayin a Nijeriya domin jana’izarsa a mahaifarsa sa ke jihar. Injiniya Kofar Marke ya bayyana baƙin ciki da rashin Abubakar Lawal, wanda ya bayyana a matsayin ɗan kwallon ƙafa na musamman kuma jakada nagari a harkar wasanni. “Labarin rasuwar nan abar girgiza da taba zuciya ce, domin marigayin ya bayar da gudunmuwa a harkaar ƙwallon ƙafa ta a-zo-a-gani a duniya...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
Tauraron tawagar Super Eagles Ahmed Musa ya buƙaci a gudanar da bincike game da mutuwar dan wasa Abubakar Lawal wanda ake zargin ya faɗo daga wani gini ya mutu a kasar Uganda. A jiya Litinin aka ba da rahoton mutuwar Lawal wanda ‘yan sandan Uganda suka ce ɗan wasan haifaffen Sakkwato ya mutu ne bayan ya faɗo daga benen wani katafaren kanti. Mayaƙan Boko Haram sun sace kwale-kwale 8 a Borno DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Cikin wani dogon saƙo da Ahmed Musa ya wallafa a shafinsa na X, ya buƙaci a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin. “Muna baƙin ciki da samun labarin mutuwar Abubakar Lawal. Wannan lamari ne...
Ana zargin malamin makarantar Aliyu Mustapha Academy da ke Jimeta a Jihar Adamawa kan wuce gona da iri da kuma azabtar da wani ɗalibinsa a dalilin shan mangwaro a lokacin ‘break’ a harabar makarantar. Aminiya ta ruwaito cewa a lokacin da ake tsaka da hutun tara ne malamin yan kama ɗalibin yana shan mangwaro, inda ya lakaɗa wa ɗalibin dukan tsiya. Shaidu sun ce har da naushi malamin ya riƙa yi wa ɗalibin, lamarin da ya sa taron ya ƙuƙƙuje tare da barin sa da tabbai a jikinsa. Malamin yana tsaka da dukan ɗalibin ne mahaifin yaron ya je makarantar domin tabbatar da biyan kudin makarantar ɗan nasa. NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Har yanzu Najeriya...
Jami’ai a yankin kudu masu yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 sun mutu sakamakon fashewar wata motar da ke ɗauke da masu haƙar ma’adinai a yankin Harnai da ke lardin Balochistan. Jami’an yankin sun ce suna ci gaba da bincike kan abin da ya haifar da fashewar, to amma ana kyautata zaton abubuwan fashewa ne da ƴanbindiga ke amfani da su. Lardin Balochistan mai albarkar ma’ainai ya shafe gomman shekaru yana fama da matsalolin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai na ƙabilar Baloch.
Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi Cikin wata sanarwa da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC), ya fitar a shafinsa na X, ya bayyana cewa matsalar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:34 na safiyar ranar Laraba. Sai dai AEDC, ya ce ana aiki tare da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dawo da wutar da...
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ’yan mata shida masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17 a yankin unguwar Pandogari da ke Ƙaramar hukumar Rafi ta Jihar Neja. Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, da tsakar daren Laraba ne ’yan bindigar suka kaiwa unguwarsu hari inda suka kashe wani ɗan banga mai suna Aliyu Aminu tare da yin garkuwa da ’yan matan. ’Yan fashin teku sun sace jirgin fasinja mutum 11 sun ɓace a Ribas Jirgin Amurka ɗauke da mutum 10 ya ɓace Mazauna yankin sun ce, maharan da suke da yawa sun shiga cikin unguwar ne daga yankin Birnin Gwari, ta Kwalejin fasaha ta Mamman Kontagora da ke Pandogari. Majiyoyi sun ce an kai ’yan matan da...
Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci hukumomin ilimi su tabbatar da cewa makarantun gwamnati da masu zaman kansu sun ɗauki matakan kare ɗalibai daga haɗura. Wannan kira na zuwa ne bayan da wata gobara ta yi ajalin almajirai 17 a wata makarantar tsangaya da ke garin Ƙauran Namoda, a Jihar Zamfara. Allah Ya yi wa Sheikh Ishaq Yunus rasuwa Tinubu ya yi sauye-sauye a Jami’ar Abuja Gobarar, wacce ta tashi da daddare a ranar Talata, ta kuma jikkata wasu almajirai bakwai, amma yanzu haka suna asibiti ana kula da su. Shugaba Tinubu ya jajanta wa Gwamnatin Jihar Zamfara da iyalan waɗanda da suka rasa ’ya’yansu a wannan iftila’in, tare da yin addu’ar samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata. Ya buƙaci makarantu...