Kotu Ta Dage Shari’ar Zargin Cin Hanci Da Ake Yi Wa Shugaban KANSIEC Na Kano Zuwa Nuwamba
Published: 22nd, July 2025 GMT
Masu ƙarar sun bayyana cewa an ce an bai wa kamfanin kuɗin ne domin samo kuɗin hannu don biyan ma’aikatan wucin gadi da aka ɗauka a zaɓukan ƙananan hukumomi na 2024. Daga bisani kuma, an ce an dawo da kuɗin a matsayin tsaba zuwa hukumar.
Lauyan ICPC, Barr. Enosa Omoghibo, ya shaida wa kotu cewa an shirya fara gurfanar da waɗanda ake zargi ne, amma “ba su halarci kotu ba.
Sai dai Lauyan waɗanda ake ƙarar, M.A. Magaji (SAN), ya ce abokan hulɗarsa ba su samu takardun shigar da ƙara kotu ba. Ya ƙara da cewa isar da takardu abu ne mai muhimmanci kafin kotu ta iya ci gaba da shari’a.
Daga nan ne kotu ta dage ci gaba da shari’ar zuwa 24 ga Nuwamba, 2025.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Farfesa Sani Lawan Malumfashi Ƙananan Hukumomi Zaɓe
এছাড়াও পড়ুন:
An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi
’Yan bindiga sun sace Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Honarabul Samaila Bagudu, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu.
Rahotanni sun bayyana cewa ’yan bindigar sun mamaye garin Bagudu ne da yammacin ranar Juma’a tare da yin harbe-harbe don tsorata al’umma.
Maharan sun yi awon gaba da ɗan majalisar ne a kan hanyarsa ta dawowa daga masallaci bayan ya an idar da sallah masallaci a garin na Bagudu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnatin Jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya ce an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da kuɓutar da Mataimakin Shugaban Majalisar.